✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarki Salman ya gana da Shugaban Amurka a Jedda

Sun tabo batun tarihin alaka tsakanin kasashen biyu.

Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdul-aziz tare da Yarima mai jiran gado, Muhammad Bin Salman sun gana da shugaban Amurka Joe Biden a birnin Jidda.

Kamfanin Dillacin Labaran kasar na SPA ya ruwaito cewa, shugaban na Amurka tare da tawagarsa sun samu kyakkyawar tarba a lokacin ziyarar tasu zuwa fadar sarkin na Saudiyya.

Yayin ganawar shugabannin biyu a ranar Juma’a, sun tabo batun tarihin alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma bijiro da hanyoyin kara inganta dangatakar da ke tsakaninsu.

Ganawar Sarkin Saudiyya da Shugaban Amurka

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai babban mai bai wa Sarkin shawara kan harkokin tsaro Dokta Musaed bin Mohammed Al-Aiban da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da Mai ba da shawara kan Harkokin Tsaro, Jake Sullivan.