✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Salman da sauye-sauyensa a shekara bakwai a kan mulki

Saudiyya daula ce ta jinkai da tausayin al’umma.

Mutanen Saudiyya da dama sun yi ta bayyana ra’ayoyinsu a shafukan sada zumunta kan cikar Sarki Salman na kasar shekara bakwai a kan karagar mulki.

A ranar Litinn 8 ga Nuwamban da ta yi daidai da 3 ga Rabi’us Sani shekara ta 1443 Bayan Hijira, Sarki Salman Bin Abdul’aziz ya cika shekara bakwai a kan karagar mulkin Saudiyya.

Mutanen kasar sun kaddamar da maudu’ai da dama a Tiwita don taya Sarkin nasu murnar wannan rana, inda suka yi ta tunawa da gagarumin ci-gaban da ƙasar ta samu a dukkan fannonin rayuwa da matakan da masarautar ta dauka don zama jagora a duniya, musamman bayan karbar shugabancin Kungiyar G20 ana tsaka da fama da cutar Coronavirus.

Da dama sun yi wa Sarkin godiya, musamman kan kokarin shawo kan yaduwar cutar Coronavirus da ta kawo cikas ga yadda aka saba gudanar da ibadar Hajji da Umara.

Duniya tana yi wa Saudiyya kallon wata kasa da ta jajirce ta ci cutar Coronavirus da yaki, ta hanyar daukar tsauraran matakan dakile cutar bayan bullarta.

Daga samun labarin bullar cutar a kasar kawo yanzu, Saudiyya a karkashin Sarki Salman ta nuna da gaske take yi wajen magance ta, inda tuni an yi wa kashi 70 cikin 100 rigakafi da suka hada da ’yan kasar da mazaunanta har ma da ’yan ci-rani da suka shiga ba bisa ka’ida ba, kuma a matakin duniya Saudiyya ta taka rawar gani wajen agaza wa sauran kasashe wajen yakar cutar.

A taron Majalisar Dinkin Duniya na 76 da aka yi a watan Satumban bana ta Intanet, Sarki Salman ya ce “Saudiyya ta taya duniya yaki da cutar Coronavirus da Dala miliyan 800.”

Ya kara da cewa “Saudiyya daula ce ta jinkai da tausayin al’umma.”

To amma ba wannan ne kadai gagarumar nasarar da za a ce Sarki Salman ya samu ba, lura da yadda ake samun haske kan shirin Saudiyya na ‘Vision 2030’, wani shiri na yi wa kasar garambawul da zai tabbatar da sauye-sauye ta fannin habaka tattalin arziki da bai wa al’umma wasu damarmaki da a baya ba a ba su.

Bugu da kari a karkashin mulkin Sarki Salman an samu sauye-sauye da ba a saba gani ba, wadanda suka janyo ce-ce-ku-ce a kasar da fadin duniya.

Sarkin mai shekara 85 ya zama sarki ne bayan rasuwar dan uwansa Sarki Abdullah dan Abdulaziz, wanda hakan ya ba shi damar zama mai kula da masallatai mafiya tsarki a duniya da ke biranen Makka da Madina.

Kafin Salman ya zama Sarki, ya zama Yarima mai jiran gado, kuma a watan Nuwamban 2011 aka nada shi Ministan Tsaro na Saudiyya.

Kuma kafin wadannan mukamai, ya shafe sama da shekara 50 a matsayin Gwamnan Riyadh.

Shi ne da na 25 ga Sarki Abdul’aziz kuma dansa na shida cikin waɗanda suka yi sarauta bayan Sarki Faisal da Sarki Khalid da Sarki Fahd da kuma Sarki Abdullah.

Tun hawan Sarki Salman bai bata lokaci ba wajen kaddamar da manyan ayyukan bunƙasa tattalin arziki da lafiya da ilimi da walwalar jama’a da sufuri da sadarwa da sauran abubuwan inganta rayuwar al’umma.

Wadannan sauye-sauye sun shiga kowane lungu da sakon Saudiyya, a waje kuma Saudiyya ta samu nasarar bunkasar tattalin arziki da ya sa ta ja ragamar shugabancin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na G20.

Sai dai mafi yawa ana ganin Yariman Saudiyya ne yake juya akalar masarautar kuma shi ke kawo sauyesauyen da yawanci ake Allah-wadai da su.

Irin wadannan sauye-sauye dai sun hada da:

1. Dage haramcin shiga sinima ga maza da mata

2. Tarurrukan casu, wadanda ko a watan Oktoban da ya gabata wani bidiyo ya nuna mata da maza sanye da kayan ninkaya suna cashewa a bakin ruwan Jeddah wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar

3. Dage haramcin tukin mata

4. Bude gidan rawa a Saudiyya

5. Bikin kafa Saudiyya da ya kawo gwamutsar mata da maza

6. Kallon ’yan kokawa na Amurka

7. Tseren keke na mata zalla da sauransu.