✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarki Charles III zai yi gwanjon dawakai 14 na Sarauniya Elizabeth II

Daga cikin dawakin har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.

Sarki Charles III zai sayar da wasu daga cikin dawakan da ya gada daga mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.

Marigayiya Sarauniya ta kasance mai son dawaki kuma tana kiwonsu.

Gidan gwanjon kayayyaki na Tattersalls ya ce zai yi gwanjon dawakai 14 na Sarauniya a yau Litinin.

Daga cikin dawakan har da Just Fine wanda ya lashe tsere kusan 100.

Kakakin gidan gwanjon na Tattersalls ya ce ba wani sabon abu ba ne saboda a duk shekara suna sayar da dawakai.

Jimmy George ya ce “wannan ba sabon abu ne, ita kanta Sarauniya ta saba kiwon dawakai sannan ta sayar, don ba zai yiwu ai ta ajiyarsu ba.”