✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Aminu ya yi sauye-sauye a Masarautar Kano

Sarkin ya ce an basu wannan rawani ne saboda cancantarsu.

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi sauye-sauye na daga darajar wasu hakimansa da kuma nada wasu sabbi.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da Abubakar Balarabe Kofar-Naisa, Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce daga cikin hakiman da aka daga darajarsu sun hadar da Sarkin Dawakin Tsakar-Gida, Alhaji Ahmad Ado Bayero zuwa Dan Iyan Kano, sai kuma Turakin Kano, Alhaji Lamido Sunusi Bayero zuwa Sarkin Dawakin Tsakar-Gida.

Sauran sun hada da Tafidan Kano, Alhaji Mahmoud Ado Bayero, wanda ya zama Turakin Kano, yayin da Dan Galadiman Kano Alhaji Haruna Rasheed Sunusi aka daga darajarsa zuwa Tafidan Kano, sai Alhaji Kabiru Tijjani Hashim Dan Isan Kano ya zama Dan Galadiman Kano.

Sauran, a cewar sanarwar, su ne Dan Lawan din Kano Alhaji Bashir Ado Bayero ya koma Dan Isan Kano, sai Alhaji Yahaya Inuwa Abbas, Dan Majen Kano ya zama Lawan din Kano.

Kazalika, sanarwar ta ce Sarkin ya nada Alhaji Ahmad Kabiru Bayero a matsayin Barde Kerarriya da kuma Alhaji Abdulkadir Mahmoud a matsayin Magajin Rafin Kano.

Da ya ke jawabi jin kadan baya nadin nasu, Sarkin ya ce an basu wannan rawani ne saboda cancantarsu da kuma hidimta wa al’umma.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci da su zamo jakadu nagari a duk inda suka sami kansu tare da ciyar da Masarautar Kano gaba.