Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya ja hankalin Shugaba Buhari kan rikicin Fulani da Yarabawa da ke faruwa a wasu sassan Najeriya.
Saraki ya yi wannan kira ne a shafinsa na Twitter bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan wa’adin barin yankin Yarabawa da wasu tsiraru suka ba wa Fulani a yankin, da hare-haren da aka kai musu a makon jiya.
- Muna kan binciken wadanda suka kona gidan Sarkin Fulanin Oyo – ’Yan sanda
- An ba makiyaya kwana 7 su bar dazukan Jihar Ondo
- Sarkin Fulanin Ilori ya kubuta daga hannun ’yan bindiga
“Na ga yadda ba wa Fulani makiyaya wa’adin barin jihar Oyo da Ondo ya jawo rikici, da kuma yadda aka kona gidan Sarkin Fulani.
“Ina jan hankalin Shugaban kasa, da ya yi amfani da duk wasu hanyoyi da suka dace don kar a bari wasu bata-gari su kawo fitina.
“Ya kamata kowa ya ba da gudunmuwa wajen kawo karshen matsalar tsaro, kuma Shugaban Kasa ya kamata ka kira kowa don magance matsalolin tsaro.
“Hadin kan Najeriya ya fi mana komai domin ba za mu so mu shiga tashin hankali a sanadin hakan ba”, cewar Saraki.
Har wa yau, ya yi kira ga Shugaban Majalisa da na Wakilai, Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila da su hada hannu wajen kawo karshen wannan rikici.
Sannan ya ja hankalin ‘yan Najeriya, da su kasance masu son zaman lafiya, don ciyar da Najeriya gaba.