✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sara-Suka ta sake kunno kai a Bauchi

Matsalar Sara-Suka wadda a baya ta gallabi al’ummar Jihar Bauchi musamman mazauna birnin jihar, ta sake kunno kai bayan da ta lafa a ’yan shekarun…

Matsalar Sara-Suka wadda a baya ta gallabi al’ummar Jihar Bauchi musamman mazauna birnin jihar, ta sake kunno kai bayan da ta lafa a ’yan shekarun nan.

Aminiya ta gano cewa a a cikin watan jiya fada a tsakanin kungiyoyin Sara-Suka da ba sa ga maciji da juna ya jawo rasuwar wani matashi a Unguwar Rijiyar Bauchi, sai kuma aka sake kashe wani matshi a Unguwar Bakin Kura sai kuma wani matashi da aka kashe a Unguwar Bakaro. Kuma a kwanakin baya ma  sai da ’yan sanda suka kama mutum 16 da ake zargin  ’yan Sara-Suka ne, ciki har da wadanda suka sassari ’ya’yan Kungiyar Mawaka ta Jihar Bauchi.

Sai dai lamarin Sara-Suka na baya-bayan nan shi ne wanda ya auku a ranar Juma’ar da ta gabata, inda matasa da ake zargin ’yan Sara-Suka ne suka kashe dan fitaccen mawakin Hausar nan Alhaji Dahiru Musa Jahun mai suna Jamilu Dahiru Musa Jahun, mai shekara 19 a garin Bauchi.

Mamacin, wanda dalibi ne da ke aji biyu a Babbar Sakandaren Jeka-ka-Dawo da ke Bauchi, ya rasu ya bar mahaifansa da ’yan uwansa da dama.

Da yake bayyana yadda al’marin ya faru ga wakilin Aminiya, dan uwan mamacin, Bashiru Dahiru Musa Jahun ya ce “Abin da ya faru da kanena shi ne, yara ne suka dauki doka a hannunsu suka kuma yi masa ta’addanci, suka hallaka shi. An ce ana biki ne, sai Jamilu ya je kallo, to sai wadanda suka hallaka shi suka je wajen. An shaida mana  cewa a lokacin da ake kallon shi marigayin wai ya karbi aron sandarsu sai yaron ya ce ya ba shi sandarsa sai ya ba shi. Bayan ya ba shi sai ya ci gaba da kunkuni. Sai kuma wadansu matasa yaran Unguwar Gwallaga suka doso wajen. Yana ganinsu ya kama kuka don ya san su, yana cewa ga wadansu suna zuwa za su hallaka shi ya gudu ya shiga wani gida yaran suka bi shi har cikin gidan suka sassare shi da adda da wuka.”

Yayan mamacin wanda malami ne a Kwalejin Koyon Ilimin Shari’ar Musulunci ta A.D Rufa’i da ke Misau ya ce sun sare shi da adda a kai, kan ya tsage. Haka kuma suka sare shi suka soka masa wuka a cinya, inda cinyar ma ta yi ta zubar da jini sosai. Aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jamiaar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, likitoci suka duba shi, suka ce ya rasu.

Ya ce bayan sun dawo da shi daga asibiti, sun kai rahoton al’amarin ofishin ’yan sanda, inda suka zo suka dauki gawar, suka yi gwaje-gwaje, suka dawo da ita; daga bisani aka yi masa jana’iza. “Muna rokon Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa,” inji shi.

Ya ce ire-iren wadannan matsaloli na matasan suna faruwa ne sakamakon gazawar gwamnati ta samar da ingantacciyar alkibla ga matasan, wanda hakan ya haifar da matsalolin rashin abin yi da kuma wahalar rayuwa. Sai ya roki gwamnati da masu hannu da shuni su kara tashi tsaye don warware wadannan matsaloli.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar kan lamarin; indya ce zai bincika kuma duk irin bayanin da ya samu zai sanar da jama’a.