✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai koma kasar waje sa’o’i kadan bayan dawowarsa

Zai yi tafiya kasa da sa'a 48 da taron zaben dan takarar shugaban kasa na APC

Sa’o’i kadan bayan dawowarsa daga kasar Spain, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, na shirin yin wata tafiya zuwa kasar waje.

Tafiyar tasa ita ce ta uku a cikin kwana takwas, inda a wannan karon zai je kasar Ghana ranar Asabar 4 ga watan Yunin da muke ci, washegarin dawowarsa daga tafiyar kwana uku a kasar Spain.

Kafin zuwansa Spain, Buhari da iyalansa sun je birnin Malabao na kasar Equatorial Guinea, inda ya halarci Babban Taron Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a ranar 26 ga watan Mayu.

Tafiyar Buharin ta ranar Asabar na zuwa Ghana na zuwa ne kasa da sa’a 48 da fara gudanar da babban taron zaben fitar da dan takarar jam’iyyarsa ta APC, bayan ta dage shi da mako guda.

Ko a lokacin da jam’iyyar ta dage gudanar da taron bayan hukumar zabe ta INEC ta kara wa’adin gudanarwa a makon jiya, shugaban kasar yana kasar waje.

Yanzu dai babban taron jam’iyyar zai gudana ne a ranar 6 zuwa 8 ga watan Yunin da muke ciki.

sanawar da kakakinsa, Femi Adesina, ya fitar a ranar Asabar ta ce, “Yau (Asabar) Shugaba Buhari zai je birnin Accra na kasar Ghana domin halartar Babban Taron Shugabannin Kasashen Kungiyar ECOWAS kan rikicin siyasar kasar Mali da wasu kasashen yankin.

“Taron da zai gudana a Fadar Shugaban Kasar Ghana zai tattauna kan nasarorin da aka samu a tattaunawar da aka yi da sojojin da suka yi juyin mulki a Mali game da maido da mulkin dimokuradiyya a kasar.

“Shugabannin za su tattauna kuma a kan halin da aka ciki a kasashen Burkina Faso da Guinea, kuma a ranar zai dawo Abuja bayan kammala taronm” inji shi.

Ya ce, ’yan rakiya sun hada da Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama da Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Ya Babagana Monguno da Daraktan Hukumar Leken Asiri, Ahmed Rufa’i Abubakar.