✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanyi: Hayakin Gawayi ya kashe miji da mata a Kano

Miji da matar sun kunna gawayin da zummar dumama daki sakamakon sanyin da ake yi.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wani miji da mata sakamakon hayakin garwashi da ya turnuke su a Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Haruna Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Kiyawa, ya ce mijin da matarsa – Suleman Idris mai shekara 28 da Maimuna Haliru mai shekara 20 – sun bakunci lahira a kokarin dumama dakinsu da garwashi wutar.

“Mun samu rahoton faruwar lamarin a ranar 3 ga watan Janairu, 2023 da misalin karfe 9 na safe cewar wasu magidanta ba su fito daga daki ba tun ranar 2 ga watan Janairu da misalin karfe 11 na dare.

“Kakar Idris ta sa an bude dakin wanda aka iske su a kwance a kan gado ba sa motsi yayin da hayakin garwashi da suka ji dumi cikin dare ya turnuke dakin.

“Bayan samun labarin, Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Mamman Daura, ya aike da jami’ai wajen karkashin jagorancin DPO na yankin, CSP Ahmed Hamza.

“An garzaya da ma’auratan zuwa aAsibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, wanda a nan likita ta tabbatar da rasuwarsu,” in ji Kiyawa.

Kakakin ya ce binciken rundunar ya gano cewar mamatan sun shiga daki da garwashi n ne da nufin jin dumi sakamakon sanyi da ake fama da shi.

“Sun rufe daki kuma ga hayakin gawayin yana tashi sannan barci ya kwashe su wanda hakan ya yi sanadiyar ajalinsu.”

Kiyawa wanda ya rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike, ya shawarci jama’ar jihar da taka tsan-tsan wajen amfani da garwashi a wannan yanayi na sanyi da aka shigo, saboda akwai yiwuwar tashin gobara idan ba a bi matakan da suka dace ba.