Gwamnatin sojin kasar Mali ta yi kiranye ga duk wakilai da jakadun kasar da ke kasashen Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) da suka goyi bayan takunkumin karya tattalin arziki da kungiyar ta kakaba wa kasarsu.
A martarnin sojojin da suka fitar da tsakar dare kafin wayewar garin Lititin, sun sanar da rufe duk iyakokin kasar ga kasashen ECOWAS da ke makwabtaka da Mali.
- Rikicin Siyasa: ECOWAS ta kakaba wa Mali sabbin takunkumai
- A wajen dan sanda na sayi bindiga saboda na rika kare kaina – Matsafi
Sojojin da a halin yanzu mulkin kasar Mali ke hannunsu sun yi suka da kakkausan lafazi kan sanya musu takunkuman da suka kira “haramtattun” da ECOWAS ta yi.
Sanarwar da kakakin gwamnatin sojin, Kanar Abdoulaye Maiga, ya fitar ta kuma yi Allah-wadai da takunkuman karya tattalin arzikin da ECOWAS ta kakaba wa kasar.
A ranar Lahadi ne dai ECOWAS ta sanya wa Mali sabbin takunkumai da nufin tilasta wa sojojin gaggauta mika mulkin kasar ga zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.
Taron na Shugabannin Kasashen Yankin Afirka ya kuma hana wa sojojin taba kudaden Mali da ke Babban Bankin Kasashe Masu Amfani da Kudin CFA (UEAMOA), in banda kudaden da za a yi amfani da su domin sayen magunguna ko kuma wasu abubuwa na bukatar gaggawa.
Taron na ECOWAS da UEAMOA ya kuma rufe iyakokin Mali da duk kasashen da ke makwabtaka da ita, tare da haramta duk wata hada-hadar kudade tsakanin Mali da sauran kasashen yankin 14.
Kasashen da ke cikin kungiyoyin biyu sun kuma sanar da janye ilahirin jakadunsu daga kasar ta Mali.