✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanya janbaki na hana daukar ciki —Masana

Wasu ayyukan yau da kulllu da ke hana mace daukar ciki.

Masana sun bayyana cewa sanya janbaki da kuma tuki babu takalmi na  daga cikin abubuwan da ke hana mata daukar juna biyu.

Shugaban Kungiyar Kwararrun Masana Magunguna ta Najeriya, Farfesa Oladapo Ashiru, ne ya bayyana haka, a wani taron bikin yaye dalibai likitoci da aka gudanar a Legas.

Ya kara da cewa wasu aikace-aikace da abubuwan da ake amfani da su na yau da kullum na hana mata daukar ciki ko kuma su sa su yin bari, kamar yadda Punch ta ruwaito shi.

Farfesa Ashiru ya ce rashin nutsuwa wajen cin abinci da tara wa kai gajiya da tukin mota babu takalmi da cin wasu nau’ikan kifi suna jawo matsala ga mahaifa har su hana haihuwa.

“Yawancin mata na amfani da jan-baki, ba su san cewa yana dauke da sinadarai masu guba mai yawa ba, musamman janbaki mai araha,” a cewar Shugaban na Kungiyar Kwararrun Masana Magunguna ta Najeriya.

Ya ce wasu abubuwan da ke hana daukar ciki sun zame wa mutane jiki, har ba sa ganin su a matsayin wata matsala.

SAURARI:Yadda yunwa ta sa likitoci yajin aiki:

Ya kara da cewa, “Wasu matan ba sa tuki da takalmi saboda suna ganin tuki babu takalmi ya fi musu sauki.

“Yawancin matan da ake yi wa dashen kwan haihuwa cikin su na zubewa bayan an yi musu allurar IVF saboda takalman tukin mota na dauke da sinadarin Antimony wanda bincike ya tabbatar guba ce ga mahaifa.

“Idan ba an cire musu Antimony din ba, ba za su iya dukar ciki ba, idan ma an samu sun dauka, zubewa zai yi.

“Sauran abubuwan da ke yi wa mata irin wannan illar su ne sinadarin zaiba wanda ake samu a wasu manyan kifaye ko kuma bankararrun kifaye masu gishiri.”

“Shi ma gurbataccen mai yana lahani ga kwan haihuwan mace ko na miji kuma yana sa mai juna biyu ta yi bari,” inji Farfesa Ashiru.

Ya kara da cewa “Shi ma feshi da maganin kwari da dagwalon danyen mai da kuma amfani da janbaki, duk suna da hadari ga lafiya.

“Yin feshi da kuma maganin kwari na iya illa ga mace mai ciki da dan da take cikin mahaifanta da ma wanda ta riga ta haifa — dukkansu gubar za ta yi wa illa,” kamar yadda masanin ya bayyana.