Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya sanar da shirinsa na soke biyan fansho ga tsoffin gwamnonin jihar da mataimakansu.
Sanwo-Olu, yayin gabatar da kasafin jihar na 2021, ya ce zai mika wa Majalisar Dokokin Jihar bukatar haka da nufin rage yawan kudaden da jihar ke kashewa wurin gudanar da gwamnati.
- Dakatar da Rahama Sadau ba zai canza komai ba a Kannywood —Farida Jalal
- An ceto ‘yan mata 26 daga hannun masu garkuwa a Zamfara
“A yunkurinmu na rage kudaden gudanar da gwamanti da kuma sadaukar da kai wurin hidimta wa al’umma, za mu turo wa Majalisa daftarin dokar biyan tsoffin gwamnoni da mataimakansu fansho”, inji shi.
Ana iya tunawa, jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu shi ne ya yi Gwamnan Jihar Legas a 1999-2007 sannan Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya gaje shi daga 2007-2015.
Daga bisani, Akinwunmi Ambode, ya kasance gwamnan jihar daga 2015 zuwa 2019 lokacin da gwamna mai ci Babajide Sanwo-Olu ya gaje shi.