✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanwo-Olu ya bullo da hanyoyi 3 na kawo wa mazaunan Legas sauƙin rayuwa

Ma’aikatan gwamnati daga mataki na 1 zuwa 14 za su fara aiki na tsawon kwanaki uku duk mako.

Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya sanar da rage kashi 25 cikin 100 na kuɗin da fasinjoji ke biya a motocin sufuri mallakar gwamnati a jihar.

Sanwo-Olu ya bayyana haka ne, a ranar Alhamis, a wata hira da ya yi da manema labarai kai tsaye a gidan talabijin na Arise.

Gwamnan ya bayyana cewa, a wani mataki na saukaka tsadar rayuwar da mazauna jihar ke fuskanta, ma’aikatan gwamnati daga mataki na 1 zuwa 14 za su fara aiki na tsawon kwanaki uku duk mako.

Sai dai ya ce ma’aikatan da ke aikin koyarwa za su ci gaba da aiki bisa doron jadawalin aiki na kwanaki biyar duk mako yayin da gwamnati za ta tabbatar da karin tallafin sufuri gare su.

Gwamnan ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta buɗe kasuwannin da za su riƙa ci a ranar Lahadi cikin akalla kasuwanni 42 da mazauna yankin za su iya sayen kayan abinci a farashi mai rahusa.

Ya kara da cewa kowane mutum na iya sayen kayan da darajarsa ba ta haura naira dubu 25 a kasuwannin da aka tanada.