✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanusi II ne Sarki ɗaya tilo a Kano — Gwamna Abba

An bai wa sarakunan da aka rushe masarautunsu sa’a 48 su tattara ina su ina su.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano.

Wannan na zuwa ne bayan Gwamnan ya rattaba hannu kan dokar da ta rushe masarautun jihar guda biyar a wannan Alhamis ɗin.

A cikin wani jawabi da ya yi wa Kanawa kai tsaye jim kadan bayan ya sa hannu kan gyaran dokar, Gwamnan ya ce hakan na nufin a yanzu a wannan jiha “Sarki ɗaya tilo muke da shi.”

“Wannan yana nufin wannan sarki shi zai ci gaba da riƙe ragama ta masarautarmu,” a cewar Gwamna Abba.

Gwamnan ya amince da dawo da Sarki Sanusi bayan majalisar da ke da alhakin naɗa sabon Sarki ta isa Fadar Gwamnatin Kano a yau Alhamis.

Aminiya ta ruwaito cewa, Madakin Kano, Yusuf Nabahani ne ya jagoranci tawagar masu naɗa sabon Sarkin zuwa Fadar Gwamnatin Kano.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kano, Shehu Sagagi ne ya tarbi tawagar masu naɗin Sarkin wadda ta ƙunshi har Makama Sarki Abdullahi.

Ana iya tuna cewa, Majalisar Dokokin Kano ce ta zartar da dokar da ra rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu a 2019.

Hakan na nufin cewa an koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zaman da ta yi ranar Alhamis.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ya nuna cewar sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano duk sun rasa kujerunsu.

Da wannan lamari, Gwamnatin Kano ta bai wa dukkan Sarakunan da aka rushe masarautunsu wa’adin sa’o’i 48 su tattara ina-su-ina-su.