✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata Lado ya zargi APC da tada rikici a Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da tada rikici a mazaɓarsa. Sanata Lado…

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar PDP, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da tada rikici a mazaɓarsa.

Sanata Lado ya bayyana zargin ne bayan da ya kaɗa ƙuri’arsa da safiyar Asabar ɗin nan a mazaɓarsa ta Ɗanmarke.

Ya ce “mun sanar da hukumar zaɓe da jami’an tsaro halin da ake ciki kuma muna sauraron matakan da zasu ɗauka.”

Sai dai da  yake mayar masa da martani, gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce duk wanda ya san tarihin zaɓe a Katsina ya san waɗanda suka yi ƙaurin suna wurin tayar da rikici.

A nasa ɓangaren, ɗan takarar jam’iyyar APC, Dr Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa shi ne zai yi nasara a zaɓen.

Dr. Raɗɗa ya bayyana hakan ne bayan da kaɗa ƙuri’arsa da safiyar Asabar ɗin nan.