✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’o’i a kasar Hausa: Wanzanci

Gabatarwa Sana’a, kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take daukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance.…

Gabatarwa

Sana’a, kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take daukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Misali, sana’ar kira.

A gargajiyance, Bahaushe yana da sana’o’in da yawansu ke da wahalar kididdigewa. Daga cikin irin wadannan sana’o’i akwai manya akwai kuma kanana. Sannan masana sun kasa su zuwa kashi uku da suka hada da sana’o’in maza, sana’o’in mata da kuma sana’o’in hadaka ko gamayya.

Sana’o’in maza su ne sana’o’in da maza zalla ne suka fi yin su. Koda an samu mata a ciki to yawansu bai kai a misalta ba. Misali, sana’ar kira, fawa da sauransu.

Sana’o’in mata kuma su ne sana’o’in da mata ne kawai suka kebanta da yin su. Idan aka ga namiji a ciki irin wadannan sana’o’i akan kira shi da Dan-daudu. Daga cikin irin wadannan sana’o’i akwai sana’ar kitso, dafe-dafen abinci da sauransu.

Sana’o’in gamayya kuma su ne sana’o’in da maza da mata suka yi tarayya a ciki. Daga cikin irin wadannan sana’o’i akwai kiwo, rokon baka da sauransu.

 

Wanzanci

Wanzanci na daga cikin dadaddun sana’o’in kasar Hausa. Sana’a ce da ake yin ta ta hanyar amfani da aska da kuma wasu kayan aiki. Sana’ar wanzanci tana da matukar tasiri a kasar Hausa. Wanzami a zamanin baya matsayinsa iri daya ne da na likita a wannan zamani da muke ciki. Ke nan ana iya cewa a da, wanzami shi ke ba da maganin cututtuka. Wanzami shi ke yin aski, zane, kaciya da sauransu.

Baya ga sana’ar aski, wanzami kan gudanar da wasu ayyuka da suka shafi kawar da cututtuka ko dai ta hanyar bayar da magani kai-tsaye, ko kuma ta hanyar tsaga jikin mutum kamar cire agalawa, balli-balli, kaho da sauransu.

Sana’ar wanzanci tana da sarki da ake kira Sarkin Aska. A cikin rukunin masu sana’o’in Hausa, babu wanda ya fi wanzami kusa da jama’a.

 

Kayan Aiki

1. Zabira: ita ce jakar wanzamai, a cikinta suke zuba dukkan kayayyakin aikinsu in ban da koko da jallon ruwa.

2. Kaho: Kaho ne na saniya ake fike shi a yi masa kofa a tsakiya.

Yadda ake yi wa mutum kaho da farko za a dora wannan kaho a jikin mutum sai a rike shi da hannu, sannan a rika zuko iska ta wannan kofa. Idan wannan kaho ya kai matakin da ya kama jikin mutum, to sai a toshe kofar da hannu sannan a kawo danko a like kofar (wannan danko kuma daga jikin bishiyar gamji ake samo shi). Can kuma bayan wani dan lokaci da ake ganin jinin ya taru a wannan wuri da aka kafa wannan kaho, sai a cire kahon, sannan a dauko aska a tsattsaga wurin. Bayan an tsattsaga wurin sai kuma a sake mayar da wannan kahon, sannan a sake zuko shi, a wannan karon jinin nan da ya taru shi ne zai fara fitowa. Idan ya sake kama jikin mutum to sai a sake barinsa na wani lokaci. Can sai a zo a cire shi a zubar da jinin da ya taru a ciki. Sannan a sake kafa shi a sake zuka. Da haka-da-haka sai wannan jini ya fice baki daya. Sannan sai kuma a kawo auduga a dan gogge jinin da yake jikin mutum. Sai kuma a kawo garin magani a barbada a kan wannan tsaga.

Amfanin kaho: Ana amfani da shi wajen cire mataccen jini ko ciwon sanyi daga jikin mutum.

3. Dogari ko Mataki: Shi kuma itace ne da ake sassake shi. Ana amfani da shi wajen danne harshe idan za a cire hakin wuya (hakin wuya wani nama ne da ke tsirowa a jikin ganda, sannan yana susar hanka. Wannan yakan saka mutum ya ji kamar zai yi amai).

4. Koshiya: Aska ce mai lankwasa wacce ake yi wa kota da itace sannan a rufe kotar da fata. Da wannan aska ake cire hakin wuya.

5. ’Yartsaga: Aska ce ’yar karama da ake amfani da ita wajen yin tsaga kamar tsagar kaho, balli-balli, tsagar fuska, tsaga kurji da sauransu.

6. Aska: Aska wuka ce ta wanzamai, da ita ake aski, gyaran fuska, kaciya da sauran ayyukan wanzamai masu yawa.

7. Auduga: Ana kuma kiran auduga da sunan kada a Hausa. Amfanin auduga a wajen wanzamai shi ne share jini. Wato da ita wanzamai ke amfani wajen share jini idan sun yi tsaga.

8. Mawashi: Iri biyu ne, akwai na dutse, sannan akwai na fata. Shi na dutse irin kananan duwatsun nan ne masu kyau da siffa ta musamman ake samu yawanci a cikin kogi ko gidin dutse. Na fatar kuwa fatar tsakiyar gadon bayan akuya ce ake yanke ta a jeme ta ana amfani da ita wajen wasa aska.

9. Isga: Jelar saniya ce ake yi mata kota da itace, kuma dukawa su yi mata rufi da fata.

10. Sabulun Salo: Ana amfani da shi wajen shasshafawa a suma idan za a yi wa mutum aski ko gyaran fuska. Babban amfaninsa shi ne yakan saka sumar ta yi laushi, sannan kuma zafin askin ya ragu.

11. Koko: A cikinsa ake zuba sabulun salon da kuma ruwa kadan a samansa.

12. Jallo: Buta ce ta duma (kwarya), a cikinta wanzamai ke dura ruwan aski.

13. Matsefata: Ana amfani da ita wajen cire sartse.

14. Ruwa.

 

Ayyukan wanzamai

• Aski

• Tsaga

• Kaho

• Kaciya

• Cire sartse

• Bayar da magani

 

Wasannin wanzamai

Wanzamai suna da kebantattun al’adunsu da suke yi a lokutan bukukuwansu, suna kuma da gangarsu ta musamman. Kurya, ita ce gangar wanzamai, bikinsu kuma ana ce da shi Wasan Aska. Idan za a yi wasan aska, akan saka rana da wuri, sai jama’a su tanadi wannan rana domin kallo, su kuma masu gudanar da wannan wasa su yi shiri. Makadin gangar wanzamai yakan je filin da za a gudanar da wannan wasa ya fara kida tun da wuri. Idan jama’a suka jiyo sautin wannan ganga, sai su rika zuwa wurin sannu a hankali suna taruwa. Bayan jama’a sun taru, su kuma wanzamai sai su zo domin gwada bajintarsu. Daga cikin abubuwan da suke yi akwai fito da aska ta yi rawa, yin kaciya ba tare da jini ya zuba ba, yin kaciya daga nesa da sauransu.

Mun dauko wannan rubutu ne daga shafin Katafaren Dakin Karatu Cikin Harshen Hausa na Rumbun Ilimi na yanar gizo