✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanannen wurin sayayya a Abuja ya yi gobara

Wani sanannen wurin sayayya a unguwar Gwarimpa, Abuja, mai suna IC World Emporia Centre, ya yi gobara a da sanyin safiyar Laraba.

Wani sanannen wurin sayayya a unguwar Gwarimpa da ke Abuja, mai suna IC World Emporia Centre, ya yi gobara a da sanyin safiyar Laraba.

Wani mai amfani da X, @Mister_Mash ya wallafa wani bidiyo da ke nuna gobarar na ci a rufin ginin a asuba.

A cewarsa, “yanzu 4:13 na asuba, IC World Emporia da ke Gwarimpa na cin wuta. Na kira layin ko-ta-kwana na @Fedfireng 0803 200 3557, sai matar ta kashe. Na kira 112, suka ce in kira 122, da na kira, suka ce in kira 112″.

Sai dai bayan sa’a guda, ’yan soshiyal midiya sun wallafa bidiyon jami’an hukumar a wurin suna kashe gobarar.

Hakan na zuwa ne sa’o’i 12 bayan fashewar wani abu da ake kyautata zaton na wasu masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne da ya yi ajalin mutum 2, wasu 77 suka jikka a Ibadan, a babban birnin jihar Oyo.

Gidaje da dama sun lalace sakamakon fashewar, wadda aka ta girgiza unguwanni da dama.