✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar walda ta fi yawon bara – Misbahu gurgu

Misbahu Ja’afar wani gurgu ne da ya kama sana’ar walda.  Ya rungumi sana’ar ce don ya rufawa kansa asiri duk da kasancewarsa gurgu dan kimanin…

Misbahu Ja’afar wani gurgu ne da ya kama sana’ar walda.  Ya rungumi sana’ar ce don ya rufawa kansa asiri duk da kasancewarsa gurgu dan kimanin shekara 25.  Aminiya ta zanta da shi, inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi rayuwarsa kamar haka:

 

Aminiya:  Za mu so ka gabatar da kanka?
Misbahu:  Sunana Misbahu Ja’afar. Ni Bahaushe ne, yanzu ina da kimanin shekara  25 da haihuwa.
Me ya ja hankalinka ka shiga sana’ar walda da kere-kere?
Misbahu:  Na tsinci kaina a wannan sana’a ce don in rufawa kaina asiri, kuma na ga sana’a ce da ta fi dacewa da ni.  Hasalima, sana’ar walda ta fi in rika yin yawon bara, don bara kaskanci ce musamman ga irinmu masu nakasa.
Akwai wanda ya koya maka wannan sana’a?
Misbabu:  Na koya ne a wajen wani maigidana a Unguwar Nasarawa da ke Kaduna.  Daga nan ne na bude shagona na kaina a yanzu.
Me ya sa ba ka rungumi harkar bara ba maimakon kama sana’a?
Misbahu:  Gaskiya yin bara kaskantar da kai ne, kuma ko a idon mutane mutum ba shi da kima.
Ka kai kimanin shekara nawa da ka koyi wannan sana’a?
Misbahu:  Akalla na kai shekara hudu zuwa biyar.
Kamar nawa mutum zai bukata idan yana son ya shiga sana’ar walda?
Misbahu:  Yana bukatar akalla Naira dubu 300.
Wadanne irin abubuwa kake kerawa?
Misbahu:  Ina kera abubuwa da dama da suka hada da kofofi da windodi da gadaje da kujerun karfe da get da sauran abubuwa.
Wace nasara ka samu a wannan sana’a?
Misbahu:  Babbar nasarar ita ce na dogara da kaina, ba na zuwa neman taimako a wajen kowa ko yin bara.
Wane kalubale kake fuskanta a halin yanzu?
Misbahu:  Babban kalubalen shi ne rashin wutar lantarki kuma ga shi ba ni da na’urar samar da wuta ta janareto.  A mafi yawan lokaci harka kan tsaya saboda rashin wuta.
Ya batun iyali, kana da aure?
Misbahu:  A’a ban yi aure ba tukuna.
Yaushe ne wannan nakasa ta same ka?
Misbahu:  Mahaifiyata ta fada min cewa tun ina dan shekara biyu wannan lalura ta same ni, bayan an yi mini wata allura.
Wace shawara za ka ba matasa?
Misbahu:  Su rungumi sana’a, don ita ce hanyar da za su bi wajen kare mutuncinsu.
Ka taba samun tallafi  daga gwamnati ko wani ko wasu?
Misbahu:  Ban taba samun tallafin kowa ba in ban da na mahaifiyata da ta ba ni wannan jari.