✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar macizai a gonar Tukur da Tukur

A gonar macizai ta Tukur & Tukur da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi, an kawata kejin macizan kuma an lailaye bangayen katangar gonar da…

 Muhammad Salisu a cikin kejin rike da macizaiA gonar macizai ta Tukur & Tukur da ke kan hanyar Abuja zuwa Keffi, an kawata kejin macizan kuma an lailaye bangayen katangar gonar da duwatsun alfarma, ga shuke-shuke da bishiyoyi iri-iri, wadanda ke sanyaya gonar, don jin dadin kowace irin halitta.
Wanda bai san wannan muhalli ba, zai tsammaci ko gidan wani hamshakin attajiri ne da ke da sha’awar zama a wurin da babu hatsaniya, amma kash! gidan kiwon macizai ne da sayar da su.
Wannan gona na da fadin hekta 20, inda aka raba ta gida biyu, a daya bangaren ana kiwon kifaye ne a kududdufai 10. A cikin gonar akwai kejin kiwon manya-manyan beraye; akwai makiyayar shanu da gonakin masara da gero da sauran nau’ukan hatsi. An kuma killace wani wuri inda ake gina makaranta da filin wasan kwallon kafa.
Jami’in kula da macizan, Muhammadu Salisu, dan shekara 25, ya kewaya da wakilanmu kowane sashe na gonar, bayan ya samu umarnin haka daga manajan gonar, Mamman Shu’aibu. Ya bude kejin farko na macizan, inda uku daga cikinsu suka yi gammo na salo daban-daban. Ya shiga cikin kejin, sannan ya bukaci wakilinmu ya shiga, ya ce masa, “Kada ka damu, muna lura da komai daga nan. Ina amfani da magani in kama su. Don haka idan ina tare da kai, ba za su cutar da kai ba. Na gaji wannan abu ne daga iyayena. Mahaifina ya sha gaya mini cewa daga sana’ar kama maciji ya biya sadakin mahaifiyata,” amma duk wadannan kalamai ba su shawo kan wakilinmu ya yarda ya shiga cikin kejin ba.
Shi kuwa manajan gonar, Mamman Shu’aibu ya bayyana suna da kejin macizai masu nagarta, don ba a so a rika cusa su a matsattsen wuri. “Yanzu mun fara kiwon kananan macizai. Muna da nau’ukan kejin macizai biyar, inda muke kula da bakin maciji da mesa da bakin mamba da saurna macizai. Mun fara wannan sana’a a cikin watan Afrilun bana, inda muka fara da macizai masu dan girma.
“Mun sayar da rukunin farko. Yanzu mun fara kiwon kanana. Mun kuma aika a kawo mana manya-manya daga wajen mafarauta da masu kama macizai. Mutane na zuwa su saya, su sanya su a keji, wasu kuwa suna saye ne don su ci. Muna kuma tura mutane su je, su kamo mana. Har yanzu ba mu taba samun wani hadari na cizon maciji ba, tun da muka fara,” inji shi.
Dangane da kiwon shanu kuwa, Mamman ya ce, “Babu irin nau’ukan shanun Najeriya da ba mu da su. Muna kiwonsu don samar da nama.”
A sashin kiwon kifi kuwa, ya ce: “Muna da manyan kifaye maza fiye da nau’uka dubu 10 na tarwada (tilapia) da manyan kifayen teku (marine fish).”