Wani matashi mai sana’ar kira a Unguwar daki-Biyu da ke gundumar Utako a Babban Birnin Tarayya, Abuja mai suna Malam Abbas Isa ’Yandadi ya ce rashin makera a yankin ne ya sanya shi kafa makera domin gudanar da sana’ar kira shekara takwas da suka gabata.
Malam Abbas ’Yandadi wanda ya fito daga garin ’Yandadi a karamar Hukumar kunci da ke Jihar Kano, ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da wakilinmu a farkon wannan mako, inda ya ce, lokacin da ya zo Abuja shekara takwas da suka gabata, ya zo ne da niyyar sana’ara kira ko wata harka ta neman arziki, amma sai ya lura babu wata makera a unguwar daki-Biyu ko kusa da ita duk da cewa akwai masu bukatar kayayyakin aiki don gudanar da sana’ar noman rani da na damina.
Abbas ’Yandadi ya ce a cikin shekara takwas da ya yi, yana kira a unguwar yakan zo ne ya yi wata biyu zuwa uku ko fiye sannan ya koma gida ya sake dawowa.
Ya ce, ba wai samun da yake yi a sana’ar ta fi ta gida ba ce, ya ce wani lokaci abin da yake samu a garinsu ya fi na Abuja, to amma rashin makera da kuma yadda mutane suke bukatar a rika sana’anta musu kayan aiki ya sanya yake zuwa ya zauna na wani lokaci yana kirar.
Ya ce, yana samun aiki daga unguwannin Lugbe da Life Camp da Utako da Mabushi da sauransu. “Sana’ar kira ta yi mini komai, da ita na yi aure kuma ina daf da sayen gida da ita. Kuma duk da cewa ina yin noma, amma na fi yin kira fiye da noma. Saboda sana’a ce da na gaje ta iyaye da kakanni.”
Abbas ’Yandadi wanda ya ce yana kera duk wani kayan aikin gona da suka hada da fartanya ta noman masara ko dawa da ta noman shinkafa ko albasa da garmuna da sauran kayan aikin gona, ya ce babbar matsalar da su makera suke fuskanta a yanzu ita ce ta rashin wata kungiya da za ta hada kansu su rika samun tallafi ko basussuka daga gwamnati ko hukumominta da bankuna domin bunkasa sana’ar ta yadda za ta tafi tare da zamani.
Ya ce watsi da sana’o’in hannu da aka gada na jawo illa a tsakanin jama’a, domin hakan yana taimakawa wajen samun matasa marasa aikin yi da suke iya zama barazana ga zaman lafiya. Ya ce raina sana’o’in da rashin wadatar zuci na daga cikin dalilan da wasu daga cikin matasa ke kin rungumar sana’o’in, “Akwai bukatar matasa su daina raina sana’ar hannu saboda akwai rufin asiri a cikinta koda mutum bai tara dimbin dukiya ba, to kuwa ba za a gan shi yana yawon maula ko gararamba a gari ba,” inji shi.
Abbas ’Yandadi ya ce, yana koyar da matasa da dama wannan sana’a ta kira, inda ya yi kira ga matasa musamman na nan Arewa su tashi haikan wajen koyon wasu sana’o’i dogara da kansu kamar kira da rini da jima da dinki da gyaran ababen hawa da sauran sana’o’i domin kare mutuncin kansu da na iyalansu.
Sana’ar kira ta yi mini komai – Abbas ‘Yandadi
Wani matashi mai sana’ar kira a Unguwar daki-Biyu da ke gundumar Utako a Babban Birnin Tarayya, Abuja mai suna Malam Abbas Isa ’Yandadi ya ce…