✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar hada carbi ta yi mini komai a rayuwa -Iliyasu Maicarbi

Malam Iliyasu Musa Lambu, mai sana’ar hadawa da shirya carbi. Yakan yi masa ado da shaida gwargwadon bukatar mai saye. Aminiya ta sami tattaunawa da…

Iliyasu Maicarbi a bakin sana’arsaMalam Iliyasu Musa Lambu, mai sana’ar hadawa da shirya carbi. Yakan yi masa ado da shaida gwargwadon bukatar mai saye. Aminiya ta sami tattaunawa da shi kan sana’ar tasa, inda a ciki ya bayyana irin alafanun da ya samu sakamakonta, kamar haka:

Ko za ka gabatar da kanka?
Sunana Iliyasu Musa. An haife ni a garin Lambu da ke cikin karamar Hukumar Tofa da ke Jihar Kano. Yanzu ina da shekara 35 a duniya. Ina da mata da yara kuma sana’ata ita ce ta shirya carbi da yi masa kwalliya. Kuma ina gyaran carbi idan ya tsinke. Ina sayarwa ga masu saye dai-dai da kuma masu sari da yawa.
Ya aka yi ka tsunduma cikin wannan sana’a?
Gaskiya ban san yadda aka yi ba, domin na tashi na ga yayyena suna yi, sai kawai ni ma na nuna sha’awar koyonta, sai yayyen nawa suka kawo ni nan Legas. A nan na koya kuma ni ma har na koya wa wasu. Saboda haka babu abin da zan ce sai dai na yi godiya ga Allah.
Ka kai shekara nawa kana sana’ar?
Gaskiya na kai fiye da shekara bakwai ina yi. Saboda tun ina matashina na fara kuma har yanzu ina yi.
Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa ka samu a cikinta?
To sai dai mu yi wa Allah godiya, don gaskiya na samu nasarori da yawa a cikin wannan sana’a, saboda a ciki nake ci nake sha kuma nake daukar nauyin iyalaina. Babbar nasarar da na samu ita ce ta rufun asiri kuma ina dogara da kaina. Na mallaki abubuwa da yawa na rayuwa. Na gode wa Allah, domin sana’ar carbi ta yi min komai a rayuwa.
Ta yaya za ka iya bayyana matsalolin da ke damunka?
Alhamdulillahi, babbar matsalar da ke damuna ita ce yadda ake kama mana mutane idan suka fita talla. Amma dangane da kayan da nake hada carbin da su ba na samun wata matsala wajen samun su. Ina samun kayan daga Jihar Kano da kuma a nan Legas. A Jihar Kano, Hausawa ne suke kawo shi, a Legas kuwa Inyamurai ne suke kawo shi.
Ko za ka iya fayyace mana ire-iren sunayen carbin da kake hadawa?
Akwai carbin da muke kira dan-Kaulaha da karaminsa da muke kira lokal da karamba da kuma sauran kala-kala kamar baki da fari da ruwan dorawa da ruwan toka da ja baki da sauransu. Sannan akwai alama da ake sanyawa. Ita muna sanya ta saboda maganin zarewar carbin. Sannan kuma akwai ’yan kirge guda goma da alamomi da ake sanyawa.
Me kake so ka cimma a sana’arka?
Ina fatan na cimma nasara a sana’ar da nake yi, babu abin da ya wuce ka samu nasara a duk abin da ka sanya a gaba. Sannan kuma ina so na cimma burin bude katafaren shago, na zama babban dila kuma ya zamana ni ma ina fita kasashen waje ina kawo carbi, ina bayarwa sari.