Wata matashiya mai sana’ar gyaran gashin mata a Abuja mai suna Blessing John, ta ce sana’ar tana da rufin asiri sosai, amma kuma ta ce babban kalubalen da take fuskanta shi ne yadda za ta rika samun karuwar abokanan hulda a kullum.
Blessing wacce aka haifa a garin Abuja kimanin shekaru 20 da suka gabata ta shaida wa Aminiya cewa mafiyawan masu zuwa wurinta don ta gyara musu gashi ba kullum suke zuwa ba.
Ta ce: “Da yawa daga cikin abokanan huldarmu ba su tsayawa wuri daya. Idan suka zo wurinka yau to gobe wani wurin za su. Wannan babbar matsala ce a gare ni. Saboda haka kalubalen da nake fuskanta shi ne yadda zan janyo hankulansu su rika zuwa wurina kawai ba tare da sun je wurin wani ba. Ka san ita sana’armu ba ta da tsayayyan farashi. Idan wani ya rage musu kudi sai kawai su tafi shagonsa ba tare da la’akari da cewar kai kana yi musu aiki mai kyau da idan wani ya gani zai yaba.”
Ta ci gaba da cewa “A yanzu ina ta tunanin dabarun da zan bullo da su wajen tunkarar wannan babban kalubalen da nake fuskanta wajen ganin cewa ina samun karuwar masu zuwa shagona tare kuma da hana abokanen huldata zuwa wani wuri.”
Blessing ta ce ta koyi sana’ar tun lokacin da ta kammala karatun sakandare a wurin wata yayarta.
To amma kamar yadda ta ce daga bisani sai ta yanke shawarar bude shagonta don neman na kanta tare da dogaro da sana’ar da ta koya ba.
“Wannan sana’ar da kake gani tana da rufin asiri. Shi ya sa tun lokacin da na koyi sana’ar nake burin ganin na bude shagona na kaina. Kuma na gode wa Allah ina ci da sha da kuma daukar dawainiyar wasu da ke kasana. Sana’ar gyaran gashi sana’a ce mai amfani sosai,” inji ta.
A cewarta babu irin salon gyaran gashin da ba ta iya ba kama daga salon gyaran gashi mai lakabin Bob Maley da Ghana Fiding da Twinsting da sauran salo iri-iri.
Ta bayyana cewa ta kan karbi daga naira dari bakwai zuwa dubu daya har zuwa dubu daya da dari biyar a kowane gayaran gashi.
A karshe ta bayyana burinta na komawa karatu don ci gaba da karatu ba tare da bata lokaci ba.
Sana’ar gyaran gashi na da rufin asiri matuka – Blessing
Wata matashiya mai sana’ar gyaran gashin mata a Abuja mai suna Blessing John, ta ce sana’ar tana da rufin asiri sosai, amma kuma ta ce…