Malam Lawal Jibrin Fulamba Malumfashi ya kasance kwararre a sana’ar aikin famfo, sana’ar da aka fi sani da Plumbing da Ingilishi. A ganawarsa da wakilinmu, ya bayyana yadda aka yi ya fara sana’ar da kuma irin muhimmancin da sana’ar take da shi ga rayuwar al’umma:
Aminiya: Tun yaushe ka fara wannan sana’a?
Na fara wannan sana’a tun a shekarar 1984 kuma na fara ne da gyara. Tafiya ta yi tafiya har al’amura suka yi girma, inda baya ga gyara da sanya kayan ruwa a gidaje da wuraren da ake bukata, sai ga shi kuma har na fara sana’ar sayar da sassan famfo da sauran kayan. Kuma kan haka har na samu abokan aiki, wato yara da nake aiki tare da su, ina koya masu aikin har su kware. A kan wannan aiki, babu inda ba mu zuwa cikin garuruwan jihar nan, har ma da wajen jihar.
Aminiya: Ka ce ka fara wannan sana’a tun daga shekarar 1984, shin ka je makaranta ne ka koya sannan ka fara ko kuwa yaya aka yi?
Ban je makarantar koyon wannan sana’a ba, ita wannan sana’a, na gaje ta ne daga wurin mahaifina. Domin kuwa a wurin shi mahaifin nawa na koyi ita wannan sana’a. Bayan na koya ina yin ta, sai kuma na ci gaba da koyar da ita ga wasu daga cikin ’yan uwa da ’ya’yan abokaina.
Aminiya: Ita wannan sana’a ta aikin famfo, mene ne tasirinta ga al’umma?
Ita wannan sana’a, farko abin da take bukata shi ne, mutum ya rike gaskiyarsa, zai samu fa’idarta. Kusan kowane gida, kowace ma’aikata da wurin zaman al’umma, ana bukatar aikin wannan sana’a ta famfo. Ko kauyen da babu wutar lantarki, suna bukatar aikinmu ta fuskar ruwan sha da sauransu. Ga batun samar da ruwan sha, da maganar tolet da wurin wanka da wurin wankin sutura ko mota da sauran dangogin abin da ake yi da ruwa; wannan sana’a tamu duk tana da tasiri a nan.
Aminiya: Kamar yadda ka ce kana koya wa yara wannan sana’a, ya zuwa yanzu ko yara nawa ka koya mawa?
Ya zuwa yanzu akwai yara 24 da na koya wa wannan sana’a. Wasu sun kama nasu wuraren suna cin gashin kansu, wasu kuma har yanzu suna tare da ni muna ci gaba da gudanar da sana’ar tare.
Aminiya: Tun da ka fara wannan sana’a, ko akwai wani kalubale da kake fuskanta?
Babban kalubalen da nake fuskanta, shi ne na fara bayaninsa da farko, wato cewa idan kana tafiyar da wannan sana’a, to ka rike gaskiyarka. Domin idan babu gaskiya ciki, to duk inda ka taso, to akwai cin mutunci, idan rashin gaskiya ya bayyana.
Aminiya: Mene ne burinka a gaba game da wannan sana’a? Ma’ana, kana da burin ci gaba da ita tsawon rayuwarka ko kuwa kana da nufin canza wata?
Gaskiya wannan sana’ar ba ta da wata nakasu, in sha Allahu ina da burin in rike ta tsawon rayuwata.
Aminiya: Me ka samu a rayuwarka ta wannan sana’a, wanda kake alfahari da shi?
Akwai abubuwa da yawa. Na farko, wadannan yara da nake koya wa wannan sana’a, wasu daga cikinsu, abin hannun da suka mallaka, ni ban mallake su ba. Bayan haka, ni kaina akwai ci gaba da na samu a rayuwa. ’Ya’yana da damansu suna manyan makarantu, kuma ta wannan sana’a nake daukar nauyinsu. Wannan shi ne irin ci gaban da na samu ko nake samu a albarkacin wannan sana’a.
Aminiya: A yayin gudanar da sana’ar nan, ko akwai wani abu da ya taba faruwa da kai, wanda ba za ka mance da shi ba?
Akwai wani abu da ya faru, wanda bai ma dade da faruwa ba. Akwai wani tankin adana ruwa, ga shi nan gabanmu da kake gani, wani mutum ne ya ba ni kudi wajen wata hudu ke nan, bisa ga irin abin da na karanta irin na jama’a; mutum zai fara kawo kudinsa, kamar ana sayar da abu dubu talatin ko hamsin, sai ya fara kawo kudi kamar rabi ya ba ka, ya zo ya amshe, sai a yi wata da watanni bai kawo ba. Daga baya sai ya kawo maka wasu daga cikin kudin, sai ya zo daga baya ya ce yana son kayan, bayan kuma farashin kayan ya tashi. Ka ji irin barazanar da muke fuskanta ta wannan bangare a sana’armu.
Aminiya: Ko akwai wani kira da za ka yi ga al’umma dangane da wannan sana’a?
Kiran da zan yi ga al’umma game da wannan sana’a ta fulamba, shi ne duk aikin da za ka ba da, ka tabbatar ka ba mutumin kwarai. Sannan shi wanda ka ba aikin, ya tabbatar da gaskiya da amana, ya tsaya tsakaninsa da Allah, ba wai ya yi yunkurin samun dukiya da aikin ba. Ya sani cewa, samun kudi ko dukiya daga Allah ne, ko ya yi aikin ko bai yi ba, idan Allah Ya nufa zai yi dukiya sai ya yi.
Aminiya: Ta bangaren gwamnati fa, kuna samun hadin kai yadda kuke bukata ko kuwa akwai wani cikas da gwamnati ke kawo maku ta wannan sana’a?
E, to, ka ga kamar ni nan, ina bugawa hannu biyu ne, ina aikin gwamnati, wato a asibitin ABU Shika, kuma ni Fulamba ne a wurin. Amma a nan Jihar Katsina, babu wani abu da nake yi tare da gwamnati.
Aminiya: Daga karshe, ko akwai wani kira gare ka ga matasa dangane da kama sana’a maimakon zaman kashe wando?
Kirana ga matasa shi ne, mutum ya dage ya nemi sana’a, wacce zai dogara da ita domin ta fisshe shi ga rayuwa; domin rashin sana’a ba karamin nakasu ba ne ga shi kansa da kuma sauran jama’a. Sana’a kowace iri ce, idan Allah Ya bud maka, koda faskare ne, Allah Ya sa mata albarka, ta nan ne za ka ci kuma ka samu rufin asiri kuma ka tsare wa gaskiyarka a wurinta.