✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sana’ar fawa a Kudu tamkar jihadi ne —Sarkin Fawa

Sarkin Fawan Obubra kuma Sarkin Yakin Hausawan Kuros Riba, Alhaji Lawan Ibrahim Isa ya ce, sana’ar Fawa ko shugabancin Fawa a Kudancin Najeriya, musamman a…

Sarkin Fawan Obubra kuma Sarkin Yakin Hausawan Kuros Riba, Alhaji Lawan Ibrahim Isa ya ce, sana’ar Fawa ko shugabancin Fawa a Kudancin Najeriya, musamman a Jihar Kuros Riba tamkar jihadi ne.

Sarkin Fawan ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kalaba, inda ya ce abin da yake nufi da jihdai ne shi ne a matsayinka na shugaban mahauta wajibi ne ka tsaya ka tabbatar da cewa naman da duk Bahaushe ko kowane Musulmi zai ci ya zama na saniya ce ko dabbar da aka halatta, kuma ka tabbatar an yanka ta kamar yadda addini ya tanada.

“Don haka, a matsayinka na shugaba dole ka yi jihadin tabbatar da cewa duk wani naman da aka san tsarkakakke ne an yanka shi ya samu shaida cikakkiya,” inji shi.

Da yake bayani kan yadda sana’ar Fawa ta shigo Kuros Riba, Sarkin Fawan ya ce sana’ar tana daya daga cikin dadaddun sana’o’in da suka fara shiga Kurmi, inda ya ce, mahauta ’yan asalin Arewa da suka shigo Kuros Riba sun iske ’yan asalin jihar su ma suna da tasu mahautar sai dai yanayin fawar ce ta bambanta da tasu.

“Eh! mun tarar da su suna da nasu mahautan da irin nasu maharba, idan sun harbo naman daji su zo su kacacccala a irin tasu fahimtar.

“Amma Fawa ta a yanka saniya a fitar da ita dalla-dalla, sai da Hausawa Musulmi suka zo daga Arewa.

“Sannan kabilun nan suka koya suka kara gogewa a harkar”, inji shi.

Matsalolin mahauta a Kudu

Da ya juya kan matsalolin da mahautan suke fuskanta ya ce Fawa a yankin Obubra da Kuros Riba aba ce mawuyaciya saboda halin da dabba ta shiga a yanzu, inda ya ce farashinta ya yi hawan da sai dai addu’a.

“Domin dabbobin daga Arewa ake kawo su, idan aka dauko su ga fitinar ma’aikata ga shingayen duba ababen hawa, kafin ka iso Kuros Riba kudin haraji da na gyaran hanya kadai sun ishe ka wahala.

Don haka kafin a zo nan abin ya kure, kashi 90 na mahauta suna fita don yi sana’ar ce kawai ba tare da suna mayar da kudinsu ba, sai dai su yi don maganin zaman banza,” inji shi.

Sarkin Fawan ya ce suna duba yiwuwar yadda a kungiyance za su nemi tallafi daga gwamnati don su kara jari, inda ya ce ta fuskar neman tallafi daga kungoyoyi ko cibiyoyin bayar da tallafi akwai wani tsari da suke gudanar da shi daidai da karfinsu kan haka.

Ya ce daga cikin nasarorin da ya samu tun daga lokacin da ya zama shugaban mahautan akwai hana zuwa ana tozarta mahauta saboda bashi.

Ta fuskar kubale kuwa, ya ce babban kalunalensu bai wuce na masu karbar kudin shiga ba da ba su da iyaka.

Sai ya shawarci mahautan Najeriya da na Jihar Kuros Riba, da su yi taka-tsantsan da dabbar da za su siya wajen sanin daga wajen wa suka siya gudun kada su fada hannun miyagu.