✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samuwar barci da mafarki a mahangar kimiyya (4)

Barci a Mahangar Musulunci Bayan bayanan da suka gabata daga masana fannin kimiyya da dabi’ar dan Adam  dangane da ma’ana da samuwar barci da abin…

Dole! Barci ko’ina ya kama sai an yi shiBarci a Mahangar Musulunci

Bayan bayanan da suka gabata daga masana fannin kimiyya da dabi’ar dan Adam  dangane da ma’ana da samuwar barci da abin da suka gano da kuma abin da ya bace musu, lokaci ya yi da ya kamata mu koma bangaren Musulunci mu ji me ya ce dangane da barci da kuma nau’ukansa da tsarin yinsa da kuma dalilan da suka sa a musulunce aka kawo yanayi da tsarin yadda ake barci.  Shin, akwai fahimtar juna tsakanin nassoshin kur’ani da na Hadisai a bangare daya; da na malaman kimiyya da fannin dabi’ar dan Adam kan abin da ya shafi barci, a daya bangaren?  Sannan mu dubi dalilin da ya sa har yanzu malaman kimiyya suka kasa gano abin da ke haddasa wa dan Adam barci a jikinsa.  Shin, a karshe, amsar za ta samu gare su ko dai kawai su sallama?  Wannan shi ne abin da za mu duba kafin mu shiga bayani kan mafarki shi kuma da yadda yake samuwa.
Barci a kur’ani
A cikin kur’ani mMai girma, malaman Musulunci suka ce Allah Ya ambaci kalmar “barci” (An-Nawm) a wurare tara da kalma daya, sannan ya ambaci nau’ukan barci guda biyar da a baya mai karatu ya karanta yanayinsu, wadanda Malaman Kimiyya suka gano daga baya sosai.  Wannan, a cewar Farfesa Ahmad BaHammaan, kwararre a fannin kiwon lafiya kuma masani a bangaren cututtukan da suka shafi barci a daya daga cikin jami’o’in kasar Saudiyya, na daga cikin dalilan da ke nuna matukar muhimmancin da addinin Musulunci ya baiwa barci a addinance.  Domin bayan yawan ambato, wanda hakan ke nuna himmatuwa da abu, ya kuma ambaci barci a yanayi akalla biyar.  Wadannan ayoyi duk suna cikin kur’ani Mai girma da muke karantawa dare da rana safe da yamma. Mu dauke su daya bayan daya mu gani:
Wuri na farko na cikin Suratul Bakara aya ta 255, wato Ayatul Kursiyyu ke nan.  A farkon wannan aya Allah Ya ce: “Allah, babu abin bautawa a bisa cancanta face Shi; Rayayye, Dawwamamme; gyangyadi ba ya kama Shi balle barci…”  A nan Allah na nuna mana girman kudurarSa ne da dawwamarSa, inda ya zama a kullum a tsaye yake wajen tafiyar da lamuran bayinSa, dare da rana, safe da yamma.  Abu na biyu da ayar ke nuna mana shi ne raunin dan Adam da cewa ba zai taba rayuwa babu gyangyadi ko barci ba.  
Sai wuri na biyu, cikin Suratul A’raaf aya ta 97, inda Allah ke cewa: “Shin, mutanen  alkaryu sun amince wa azabarMu ta je musu da dare, alhalin suna barci?”  Wannan aya ita ma tana nuna mana karin raunin dan Adam ne da nuna cewa barci dabi’arsa ce, kuma a sadda yake barci, rauninsa na kara ninkuwa ne, sai yadda aka yi da shi.
Sai wuri na uku cikin Suratul Anfaal aya ta 43, inda Allah ke cewa: “A lokacin da Allah ke nuna maka su suna kadan, a cikin barcinka…”  Wannan aya ta zo ne cikin jerin ayoyin da ke bayani kan abin da ya faru lokacin yakin Badar da cewa Allah Ya nuna wa Manzon Allah adadin kafirai cikin mafarki, amma sai aka ambaci barci, saboda mafarki na samuwa ne cikin barci.  
Sai wuri na hudu cikin Suratul Furkaan aya ta 47, inda Allah ke cewa: “Kuma Shi ne Wanda Ya sanya muku dare ya zama tufa, kuma barci ya zama hutu…”  Wannan aya na nuna mana cewa barci na cikin ni’imomin Allah ga bayinSa, domin lokaci ne da jikin dan Adam ke sake sabunta yanayinsa baki daya, kamar yadda likitoci suka tabbatar.
Sai wuri na biyar, cikin Suratur Ruum aya ta 23, inda Allah ke cewa: “Kuma daga cikin ayoyinSa akwai barcinku cikin dare da yini…”  Wannan ma tana magana ne kan cewa lallai barci ni’imar Allah ce ga bayinSa.  
Sai wuri na shida cikin Suratus Saaffaat aya ta 102, inda Allah ke cewa: “To, a lokacin da ya isa aiki tare da shi, sai yace: ‘Ya karamin dana! Lallai ne na gani a cikin barci lallai ina yanka ka…”  Wannan ayar na bayani ne kan dalilin da ya sa Annabi Ibrahim (AS) ya yi yunkurin yanka dansa Annabi Isma’il, amma daga baya Allah Ya fanshi dan.  Abin da ayar ke fa’idantarwa dangane da maudu’in zancenmu shi ne, ta hanyar mafarki Allah Ya umurci Annabi Ibrahim ya yanka dansa, kuma wannan, kamar yadda muka sani, shi ke nuna cewa lallai barci na daga cikin hanyoyin da Allah ke yi wa Annabawa da Manzanni wahayi, tunda ga shi har ya yi azama zai aiwatar da abin da ya gani.  
Sai wuri na bakwai cikin Suratuz Zumar aya ta 42, inda Allah ke cewa: “Allah ne ke karbar rayuka a lokacin mutuwarsu da wadannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu…”  Wannan ayar na cikin ayoyi masu dauke da babban abin al’ajabi dangane da barci da hanyar yinsa.  Bayani zai zo kan al’amuran da suka shafi sakon da ke cikinta nan gaba.  A takaice dai mun fahimci cewa Allah Ya ambaci barci a cikin wannan da cewa yana karbar rayuka a lokacin barci.  
Sai wuri na takwas a cikin Suratul kalam aya ta 19, inda Allah ke cewa: “Wani mai kewayawa daga Ubangijinka ya kewaya a kanta (ya kone ta), alhalin suna barci…”  A nan Allah na ba mu kissar wasu samari ne marowata da babansu ya mutu, alhali mai karamci ne shi, su kuma suka sha alwashin hana zakka da hana masakai daga abin da suka gada na amfanin gonar babansu, amma kafin su girbe, sai Allah Ya aika Mala’ika ya kone ta cikin dare, sannan suna barci.  Wannan ke nuna karin raunin dan Adam sadda yake barci da kuma cewa yadda Allah ke da iko a kan shi sadda yake farke, haka ake da iko a kan shi sadda yake barci.  
Sai wuri na karshe a cikin Suratun Naba’i aya ta 9, inda Allah ke cewa: “Kuma muka sanya barcinku hutawa…”  Wannan ma kari ne kan sauran ayoyin da ke bayanin ni’ima da ke cikin barci da Allah Ya samar wa dan Adam.
Wadannan su ne wurare tara da Allah Ya ambaci barci da suna daya a Larabce, wato “An-Nawm.”  Wannan kalma, inji malamai, na magana ne a kan barci a sake, ba tare da wani kaidi ba.  Amma dangane da abin da ya shafi nau’ukan barci kuma, suka ce su ma Allah bai bar su ba, sai da ya ambace su a cikin kur’ani.

Nau’ukan Barci a kur’ani
A baya mai karatu ya ji cewa akwai nau’ukan barci guda biyar, wadanda aka samo su daga kalolin barci guda biyu, wato barci mai nauyi da barci madaidaici.  Wadannan nau’ukan barci ba haka kawai masana kimiyya suka tashi suka ambace su ba, sai da suka kwashe shekara da shekaru da karni da karnoni suna bincike, cikin wahala da nishadi, cikin sanyi da zafi, kafin suka gano su.  To amma duk da wannan dawainiya da suka yi, tuni Allah Ya ambaci wadannan nau’ukan barci. Sai dai da yake galibin masu wannan bincike ba musulmi ba ne, ba lallai ba ne hankalinsu ya zo kan wadannan ayoyi. Kuma ko da hankalinsu ya zo kan ayoyin ma, ka’ida ce irin ta malaman kimiyya, cewa abu kaza ne, bai sa su yarda, sai sun gudanar da bincike. To, a ina Allah Ya ambaci wadannan nau’ukan barci guda biyar?
Wuri na farko da Allah Ya ambaci nau’in barci na farko na cikin Suratul Bakara dai har wa yau, cikin Ayatul Kursiyyu, wato aya ta 255 ke nan, inda Allah ke cewa: “…gyangyadi ba ya kama Shi balle barci…”  Malaman kimiyyar dabi’ar dan Adam suka ce a nan an ambaci gyagyadi da kalmar “Sinah,” don shi ne mafi karancin nau’i ko matakin barci.  Wannan matakin farko ke nan cikin nau’ukan barci mai nauyi, idan masu karatu basu mance ba.  Sai wuri na biyu, inda aka ambaci mataki na gaba, wato gyangyadi mai dan zurfi.  Wannan na cikin Suratu Aal Imraan aya ta 154, inda Allah ke cewa: “…sannan (Allah) Ya saukar a kanku bayan bakin ciki, wani aminci (a halin) gyangyadi da ke lullube wani bangare daga cikinku…”  A nan Allah Ya yi amfani da kalmar “Nu’ass” ne, wadda aka samo asalinta daga kalmar “An-Na’ass.”  Wannan aya na ishara ga abin da ya faru ne lokacin Yakin Uhudu, sadda wasu daga cikin Sahabbai (Allah Ya kara musu yarda) suka gudu suka haura saman tsaunin Uhudu, amma a karshe Allah Ya dora musu wani dan gyangyadi, don samun nishadi da kuzari.  Haka ma a cikin Suratul Anfaal aya ta 11 Allah Ya sake sanar da mu yadda Ya saukar da gyangyadi makamancin wannan ga Sahabbai sadda aka zo Badar, kafin a fara gwabzawa.  A nan malaman kimiyya suka ce wannan gyangyadi ya taimaka wa Sahabbai ne wajen rage gajiya da kuma samun natsuwa.  Shi ya sa ma suke cewa duk wanda ke yin barcin rana (kailula) na tsawon minti 10 akalla, kowace rana, to zai samu kuzari da kuma kaifin basira, sannan yana taimakawa wajen rage hauhawar jini (High Blood Pressure).  Wadannan nau’ukan gyangyadi guda biyu su ne matakan barci mai nauyi na daya da na biyu, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.
Sai wuri na uku da ke cikin Suratul Kahfi aya ta 18, inda Allah ke cewa: “Kuma kana zaton suna farke, amma barci suke yi…”  Wannan daya ne daga cikin ayoyin da ke bayanin yanayin da Samarin kogo suka shiga, tsawon shekaru 300 ko sama da haka. Kalmar da Allah Ya yi amfani da ita ita ce: “Rukood” wacce aka samo asalinta daga kalmar “Ar-Rakdu,” wadda ke nufin barci mai tsawo. Kamar yadda masu karatu suka sani, wadannan samari sun yi shekaru 300 ne da ’yan kai suna barci, don haka aka yi amfani da kalmar “Ar-Rukood,” wadda ke ishara ga barci mai tsawo.  
Sai wuri na hudu da ke cikin Suratuz Zaariyaat, aya ta 17, inda Allah ke cewa: “(Mumminai) Sun kasance kadan cikin dare suke barci…”  A wannan aya Allah Ya yi amfani ne da kalmar “Al-Hujoo’”, wadda ke nufin “Barcin dare.”  Wannan na daya daga cikin matakan barci biyar da bayaninsu ya gabata.
Wuri na karshe na cikin Suratun Naba’i, aya ta 9, inda Allah ke cewa: “Kuma muka sanya barcinku hutawa.”  Haka ma a cikin Suratul Furkaan aya ta 47, Ya yi ishara da cewa Ya mayar da barci ya zama hutawa ne.  Malamai suka ce a nan Allah Ya nuna cewa Ya mayar da barci ya zama hutawa, Ya kuma yi amfani da kalmar “Ja’ala,” wacce a ka’idar Larabci idan ta zo kafin kalma, takan yi aiki ne a kan sunaye biyu.  Idan haka ta kasance kuwa, to ana nufin sunan farko ne aka juya shi zuwa suna na biyu.  To me ya sa Allah Ya yi amfani da kalmar “As-Subaat” da nufin barci?  Farfesa Ahmad BaHammam ya ce saboda kalmar “Subaat” asalinta daga kalmar “As-Sabt” ne, wadda ke nufin “Yankewa daga wani abu.”  Ya ce a nan ana ishara ne zuwa ga nau’in barci mai zurfin gaske ne, wanda ke yanke zatin dan Adam daga harkokin duniya gaba daya, wanda kuma hakan ne ke haddasa masa samuwar hutu, kafin lokacin farkawarsa ta yi.
Daga bayanan da suka gabata, mai karatu zai ci karo da kalmomi guda biyar masu ishara zuwa ga nau’ukan barci biyar.  Wadannan kalmomi kuwa su ne: “Sinah,” da kalmar “Nu’ass,” da kalmar “Rukood,” da kalmar “Hujoo’,” sai kuma kalma ta karshe, wato “Subaat.”  Farfesa Ahmad BaHammaam ya ce wadannan su ne nau’ukan barci biyar da malaman kimiyya suka tabbatar a bincikensu.  Ya ce mai barci na farowa ne daga matakin “Sinah,” ya shiga matakin “Nu’ass,” ya kai matakin “Hujoo’,” daga nan sai ya haura matakin “Rukood,” kafin ya tuke a mataki na karshe, wato “Subaat” ke nan.