Akawai samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya da suka baibaye lalitar gwamnatin Haurobiya, don haka ban yi mamakin yadda jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka tara wa Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki gararuwar Hauro gashin bala karamin lauje da sili, alhali gama-garin al’umma na fama da sasarin talalar talauci, har wasu ma sun zama ja-ni-talau da dan wuya kamar rakumi-rakumi zololo. Wani abin takaici dai shi ne, mafi yawan samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya da ke wawushe asusun al’umma, tarin Hauron da suka haure da shi tamkar kudin ludi ne. Domin ba za su amfane su ba, kuma sun hana su amfani wasu.
A daidai lokacin da na dora fekakkkiyar gambata don kattaba muku darasin wannan mako, sai na ci karo da wani batu mai taken “An lamushe Hauro tiren taliya sili da sili da gashin balam kwanciyar magirbi a mulkin Gudun-loko da Jonata-tantin mulki. Wanda duk ke inkarin wannan batu da na bijhiro da shi, to sai ya lalubi shafukan yanar sadarwa na ‘Fuskantar-bokoko,’ inda wani mai kalume-kalumen bayanai ya alkinta kiyasin jaridar Ingilishi ta Fanco, wadda ta bijiro da yadda aka arce da Hauro tiren taliya babban lauje a mulkin gwamnati mai ci. Sannan abin mamakin, wannan kiyasi, a cewar mai watsattsake a shafukan fuskantar-bokoko, an tattara su ne cikin shekara ta dubu karamin lauje da sili da karamin lauje. Don haka sai ya yanke cewa, tabbas a wannan shekara ta dubu karamin lauje da sili da tsayuwa bisa kafa daya, tabbas yawan Hauron da aka haure da su har zuwa cikin shekarar da ta arce ya rubanya hasashen masu watsattsake a mujallu da jaridu.
Fashin bakin yadda aka kalumo wadannan alkaluman samartakar kusu da lakume kudin lukudi, shi ne, Rubdugau tsohon Gogarma, wanda ya yi gwagwarmaya da masu fashi da mukami ko da dabara, ya fasko sabi zarce da aka yi da damin Hauro tiren taliya sili da gashin balama dari karamin lauje a kowace shekara, inda a shekara tsayuw abisa kafa daya, aka yi gangamijon damin, sai suka tashi Jimla wahida, Hauro tiren-taliya babban lauje da gashin balama tsayuwa bisa kafa daya.
Rubdugau dai ya karkare batutuwansa da cewa a kalla Hauro tiren taliya karamin lauje da gashin bala manuniyar sama aka wawure na talalfin sudin man tunkuza.
Shi ma Masanin Sisi-da-sisi, tsohon Gwamnan Babban Asusun Haurobiya, wato Maimartaba Babban Mutum mai rawani na birnin Dabo, ya baza wa duniya yadda gafiya ta tsere da Hauro tiren taliya kofar hanci da gashin balama kwanciyar magirbi. Wannan tonon silili da ya yi, shi haifar da babbar jimurda a tsakaninsa da shugaban Jona-tantin mulki, musamman ganin cewa yana neman taka masa burki a irin gudun-lokon da aka yi da al’umma.
kwararun masana Tarawa da kwashewa da nunnunkawa da rarrabawa duk sun yi ittifaki kan cewa, an tattara Hauro tiren-taliya sili da sili da gashin balama kwanciyar magirbi, sannan aka kwashe nunkin ba nunkin, aka kuma rarraba su a tsakanin samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya.
’Yan makaranta ya kamata ku fasko cewa, a wannan jaddawalin duk ba a bijiro da wawure-wawuren da Araruma da Santala kwaiduwa, wadda ta kudundune Hauro gashin balama kofar hanci da karamin lauje suka yi ba. Ga fancon da aka yi wa tsofaffin ’yan kwadago na Hauro gashin balama karamin lauje da kwanciyar magirbi da kofar hanci.
Haurobiyawa na daina wannan kiddigar Duna ko kidayar Ingarman mutanen Autan Bawo. Domin yau a kasar Haurobiya, mutane irin su Gwamna mai sunan Sulalla na Jihar Jijjiga-ciyawa, wanda ’yan lelensa na cikinsa ke fuskantar tuhuma wawurar dukiyar talakawa da yi wa marasa galihu kisan gilla, wai su ne mutane. Mai sunan Sulalla ya sulale da sulallan al’ummar Jihar Jijjiga-ciyawa, shi ya sa ya ke ta kokarin yin karfa-karafa ya kakaba wa al’umma Rungumar rigima a matsayin gwamna gwarangwam, karkashin tutar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Duk wannan yana yi ne don kada a yi masa tonon silili kan irin ta’asar da ya tafka a kwanon tasarsa. Na-kwadi ya kare wa dan kada, domin kunya dai sai an ji ta. Ga su Malam Ya-isa-ya yi guda, Gwamna gwarangwam a Jihar Baubawan-cici, shi ma yana neman jawo muku ciwon tautau, kodayake ai ga Jatau Mai magani, af! ashe mugun gani ne!
Ita kuwa Shamuwar Jihar dakin-kara, so take yi ta yi kakara da Mai hannu da shuni, amma talakawa sun turo Mai-sare-sare zai sare su. Mutanen Birnin Dikko sai ku yunkura, don kada a hana ku laluben na-koko.
Haurobiyawa dole ne a ba mu katin zabi-sonka, musamman a Arewacin Haurobiya, domin idan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta fasko cewa karshen samartakar kusu da ’yan matancin jaba da gafiya ya zo karshe, suna iya dakile rabon kati, don su samu ci gaba da kama karya-tauna-cinye-ka-hadidiye.
karshe tika-tika tik! Ina fatan kowa ya fasko jirgin Samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya. Wannan na nuni da cewa Samarin shaho da ’yan matan kasar Niyyar-jari ke yi wa waka sun fi samarin kusu tausayi. Domin su yawon-dara suke yi da kwanyar adon-gari, su jefa su a cikin garari, amma ba su cika yin sabi zarce da damin Hauro ba. Samarin kusu masu kudin lukudi ne, sun kankane komai, sun hana al’umma su amfana da albarkatun kasar su. Haurobiyawa dai sun gaji da mai dan boto da sanda jirge. Mun gaji da ’yan gyare-gyare irin gyare da kurege; mun kosa da cin-duhu a cikin duhun dundumdurundum; uwa-uba ga yamutsin haramta bobo da kwambon boko. Don haka a zabi-sonka na shekara ta dubu karmin lauje da sili da babban lauje zabi ya rage ga mai shiga kwakware!
Samartakar kusu ko lukudi?
Akawai samarin kusu da ’yan matan jaba da gafiya da suka baibaye lalitar gwamnatin Haurobiya, don haka ban yi mamakin yadda jiga-jigan jam’iyya mai dan…