Hukumomi a Dimokuradiyyar Congo sun tabbatar da mutuwar sama da mutum 50 sakamakon hatsarin jirgin ruwa da ya faru.
Kakakin Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwan Kasar, Jose Misiso, ya ce mutane da dama sun bace.
- Tun 2016 aka san COVID-19 za ta bulla, amma aka yi sakaci
- ’Yan sanda sun kwato mutum 187 daga hannun ’yan bindigar Zamfara
Jirgin ruwan da aka makare shi da mutane fiye da kima, ya yi hatsarin ne bayan ya taso daga yankin Bumba zuwa Arewacin Mongala a ranar Laraba.
A cewar kakakin, an yi nasarar ceto mutum 30 tun bayan faruwar hatsarin.
Sai dai ya ce har yanzu ba a samu tabbacin adadin mutanen da suka bace ba.
Hukumomin kasar sun kuma bayyana cewa mutum 75 ne ake tunanin sun bace, yayin da kuma wanda suka kubuta suka shaida cewa jirgin ruwan na dauke da mutum 400 kafin ya yi hatsari.
Mutane da dama a kasar ta Congo sun koma amfani da jiragen ruwa a matsayin ababen sufuri, sakamakon, lalacewar da titunan kasar suka yi.
Sai dai a lokuta da dama ana samun mutane fiye da kima a jiragen ruwan da suke sufuri a kasar, wanda hakan na iya haddasa hatsari a lokuta da dama.