✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sama da mutum 10 sun mutu a hadarin mota a Akwanga

Wani mummunan hadarin mota da ya faru a Karamar Hukumar Akwanga jihar Nasarawa ya yi sanadiyyar rasuwar sama da mutum 10 tare da jikkata wasu…

Wani mummunan hadarin mota da ya faru a Karamar Hukumar Akwanga jihar Nasarawa ya yi sanadiyyar rasuwar sama da mutum 10 tare da jikkata wasu da dama.

Hadarin ya faru ne a wani tsauni da yake gain, wanda ya rutsa da wata motar tirela dauke da siminti da wasu motocin fasinja.

Jami’an Hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya FRSC, da sojoji da kuma ‘yan sand sun taimaka wajen taimakon wadanda hadarin ya rutsa da su.

Kwamandan FRSC na jihar Nasarawa, Ismaila Kugu, ya tabbatar da aukuwar hadarin na yau.