✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salman Rushdie: An kai wa mutumin da ya yi batanci ga Annabi hari

Ya zuwa yanzu ba a san halin da yake ciki ba.

An kai wa Salman Rushdie hari bayan ya shafe tsawon shekaru yana buya sakamakon batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

An kai wa fitaccen marubucin hari, wanda aka kwashe shekaru da dama ana yi wa barazanar kisa bayan ya rubuta littafin The Satanic Verses.

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa an kai masa harin ne safiyar Juma’ar nan yayin da yake jawabi a wurin wani taro a Yammacin Jihar New York da ke Amurka.

Marubucin, wanda ya lashe kyautar The Booker Prize, yana jawabi ne a Cibiyar Chautauqua yayin da aka kai masa hari.

Ganau sun ce sun ga wani mutum ya ruga a guje ya hau kan dandamalin da marubucin yake jawabi, inda ya rika naushi yana kuma daba wa Mista Rushdie wuka a yayin da ake gabatar da shi gaban jama’a.

Yadda ma’aikatan agajjin gaggawa suka kai wa Salman Rushdie dauki

Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet ya nuna mahalarta taron sun ruga a guje kan dandamalin don kai masa dauki.

Bayanai sun nuna cewa akwai alamun an daba masa wuka a wuya, wanda ya zuwa yanzu ba a san halin da yake ciki ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaiyo ’yan sanda na cewa an daba wa wani mutum wuka amma sun ki cewa komai game da ko wane ne

Marubucin dan asalin India ya shahara ne bayan ya rubuta littafi mai suna Midnight’s Children a shekarar 1981, wanda aka sayar da kwafi fiye da miliyan a Birtaniya kadai.

Sai dai littafi na hudu da Mista Rushdie ya rubuta a 1988 – The Satanic Verses – ya tilasta masa shiga buya tsawon shekaru tara.

Littafin ya gamu da fushin Musulmai, wadanda ke ganinsa a matsayin batanci ga addini, inda aka haramta sayar da shi a wasu kasashe.

BBC ya ruwaito cewa, shekara daya bayan wallafa littafin, Shugaban Addinin Iran, Ayatollah Khomeini ya sanya ladan dala miliyan 3 ($3m) ga duk wanda ya kashe Mista Rushdie.

Mutane da dama ne suka mutu sakamakon tarzomar da ta barke kan wallafa littafin, ciki har da wasu da suka fassara littafin zuwa wasu harsunan.