Wata gidauniya a kasar Iran ta karrama matashin nan da ya kai hari ga marubucin nan da ya i batanci ga Manzon Allah (SAW), Salman Rushdie.
Gidauniyar mai bibiyar da kuma dabbaka fatawowin Imam Khomeini, ta karrama matashin ne saboda bajintar da ta ce ya nuna inda ta ba shi kyautar filin noma mai fadin mita 1,000.
- An cafke likita kan kashe marasa lafiya da cire sassan jikinsu
- NAJERIYA A YAU: Shin Kuri’un ’Yan Najeriya Za Su Yi Tasiri a Zaben 2023?
A watan Agustan bara ne matashin wanda mabiyin Darikar Shi’a ne a Amurka ya kai wa Rushdie farmaki a wurin wani taro a birnin New York.
Harin ya yi sanadiyar Rushdie ya rasa idonsa daya, haka ma hannunsa daya ya daina aiki.
Harin na mazaunin aiwatar da fatawar da tsohon Shugaban Shi’a, Ayatollah Ruhollah Khomeini ya bayar ne na zartar wa Rushdie hukuncin kisa, shekaru 33 da suka gabata.
A wancan lokaci, Khomeini ya yi kira ga Musulmi da a kashe marubuci Rushdie saboda wani littafi da ya rubuta mai suna ‘The Satanic Verses’, wanda a cikin littafin ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW).