Bayan kammala azumin watan Ramadan na kwanaki 30, a yau al’ummar Musulmi a jihar Borno, sun bi sahun sauran takwarorinsu a jihohi daban-daban wajen gudanar da Sallar Idi.
A da dai an yi tsammanin ba za a yi Sallar Idin ba, saboda halin dokar kulle da jihar ta fuskanta har tsawon mako uku, amma bayan da kwamitin hana yaduwar coronavirus ya gana da Mai Martaba Shehun Borno da kuma limaman masallatan Idi, aka cimma matsaya a kan gudanar da Sallar a gurare da dama.
Wuraren da aka yi sallar dai sun hada da Babban Filin Idi da ke filin sukuwa, Police Ground, Federal Lowcost, Gonimi da dai sauran masallatai.
- HOTUNA: Yadda Sallar Idi ta gudana a sassan Najeriya
- Mazauna Abuja sun yi tururuwar zuwa Idi a jihar Nasarawa
Sai dai duk da umarnin da kwamitin ya bayar na kada a yi cunkoso, hakan bai yi tasiri ba, domin kuwa a duk kusan inda aka gudanar da Sallar Idin, jama’a sun cika makil, babu masaka tsinke.
A Babban Filin Idi na Maiduguri, a cewar Malam Ali Suleiman, wani bawan Allah da ya yi sallar a can, jama’a sun fito, kuma an gudanar da sallah lafiya, amma batun wani ba da tazara a tsakanin masu sallah sam babu shi.
Babu batun rufe fuska
“Haka ma babu wata takura a kan sai ka saka kyallen rufe fuska, illa idan za ka shiga za a ce maka idan kana da hankici ka rufe fuskarka, shi ma babu wanda ya matsa.
“Haka sinadarin wanke hannu, duk babu tilas a kai, kai ka ma rantse cewar babu wata doka a kan hakan, don kariya daga cutar corona, kuma gaskiya jama’a sun cika makil”, inji shi.
Dala Kolomi wani dan jarida da shi ma ya yi sallah a Babban Masallacin ya kara tabbatar da maganar cewa babu wani abu mai kama da ba da tazara: “An hada sahu kamar yadda aka saba, aka gudanar da sallah”.
Sai dai a masallacin Juma’a na El-Kanemi wanda nan ma aka gudanar da sallar Idin, wani da ya kasance a gurin, Ibrahim Uba, ya shaida wa wakilin Aminiya ta waya cewa hakika an bi dokokin da kwamitin ya umarta, kamar na wanke hannu kafin shiga harabar masallacin, sa kyallen rufe fuska – “wanda kusan kowa ka gani a gurin yana sanye da shi” – da kuma ba da tazara a tsakanin masu sallar.
A masallacin El-Kanemi
“Hakika lamarin ya burge ni, ganin yadda jama’a suka ba da hadin kansu”, inji Ibrahim.
A cewar Muhammad Sani Kawu wanda ya yi sallar Idi a Gonimi, babu wani abu mai kama da ba da tazara a tsakanin masallata, haka batun kyallen rufe fuska.
“Kashi 98 cikin 100 na wadanda suka yi sallar ba sa sanye da shi a fuskarsu, haka babu wani abin wanke hannu da aka tanadar don masu shiga su yi sallah”, inji shi.
A zagayen da Aminiya ta yi a cikin gari ta ga jama’a na ci gaba da gudanar da harkokinsu, sai dai an dan takaita zirga-zirgar ababen hawa, tun daga karfe 7 na safe zuwa 12 na rana.
Amma wannan bai hana jama’a yin tururuwa zuwa sallar Idi ba.
Jama’a na kai kawo
Duk da dai babu bukukuwa, jama’a na kai kawo da kuma ziyara ga ’yan uwa da abokan arziki.
Haka kuma duk da halin kunci da jama’a suke ciki, magidanta sun yi bakin kokarinsu wajen yin cefanen sallah, amma batun kayan salla, yara da yawa sai hakuri suka yi.
Wani yaro mai suna Abdullahi Muhammad ya bayyana cewa a gaskiya tun da aka haife shi, “a kowacce shekara iyayena sukan dinka min kayan sallah kamar uku zuwa hudu, amma a bana saboda halin da muka tsinci kanmu a ciki ko daya wallahi ban samu ba, sai dai ina godiya ga Allah da ya kawo ni wannan lokacin cikin koshin lafiya”.
Hussaini Ali Kura, wani magidanci, ya bayyana wa Aminiya cewa saboda halin matsi, ya kasa cefanen abinci a gidansa, amma dai sai godiya tun da anyi sallar lafiya.