Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i yayi watsi da bukatar da tawagar limamai da malaman jihar Kaduna, ya hana a fita ranar Asabar, ranar da ake saran za a yi idin sallah karama.
A ranar lahadi, 17 ga watam Mayu, tawagar limamai da malaman suka bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta duba yiwuwar sassauta dokar kulle a jihar domin rage wa al’umar jihar wahalhalun da suke ciki.
A sanarwar da limaman da malaman suka fitar, sun jadadda mahimmancin lura da mataken kare yaduwar cutar COVID-19 a lokacin da suka bukaci a duba yiwuwar sassauta dokar kullen domin jama’ar jihar su sami sa’ida.
Haka zalika sun yaba wa gwamnatin jihar bisa kwararan matakan da take dauka domin kare yaduwar cutar a jihar Kaduna.
Wani mataki da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka a ranar lahadin bayan bukatar malaman shine sauya ranaikun da a baya ta baiwa jama’ar jihar fita domin su sami zarafin sayan kayayyakin masarufi.
Sanarwar da manajan mai bada umarni na masana’antar da ke kula da ci gaban kasuwannin jihar Kaduna (KMDMC) Muhammad Hafiz Bayero, ya shaida cewa and sauya ranakun sassauta dokar zuwa ranar Laraba da Alhamis.
” Mazauna jihar Kaduna za su sami damar fita kasuwannin da ke kusa dasu a ranar Laraba zuwa Alhamis,20 zuwa 21 da ga watan Mayu, domin su sayi kayan abinci, da sauran mahimman kayayyakin masarufi.
“Wannan sauyi ya nuna cewa babu kasuwar da za a bude a ranar Asabar” Inji shi.
Muhammad Hafiz Bayero ya kara da cewa za a bude kasuwannin na musamman ne daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma a ranaiku biyu da za a sassauta dokar kullen, inda ya bukaci jama’ar jihar da suyi biyayya ga matakan kariya da gwamnatin jihar ta ayyana.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da tawagar limamai da malaman jihar kaduna ta bukaci sassauci a dokar kullen domin samawa al’umar jihar sa’ida.