✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sallama: Kalmomin “Ta’ala” da “Amin” kirkira ne a cikinta (1)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode MaSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa. Muna…

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode MaSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa. Muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).

Bayan haka, lallai mafi gaskiyar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), mafi kyawun shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammadu (Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam). Kuma mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkira a cikin addini, kuma duk abin da aka kirkira a cikin addini bata ne, wadda karshenta wuta. Allah Ya tsare mu daga gare ta, amin.
Bayan haka, yau mukalar tamu za ta yi tsokaci ne kan sallama da abin da ya shafe ta dangane da yin ta da amsa ta idan an yi ta. Zan yi dan kokari ne wajen nuna rashin ingancin sanya kalmar “Ta’ala” da kuma ta “Amin” wajen yi da kuma amsa sallamar, lamarin da mafi yawa daga cikin Musulmi suke aikatawa, alhali ba wata damuwa da ke bayyana gare su kan yin hakan. Hasali ma da yawa suna ganin daidai ne, babu wani abin damuwa a ciki, musamman ma ga wadanda yin bidi’a a cikin addini bai dame su ba.
Zan so, bayan an karanta wannan mukala, a samu wanda zai shiryar da ni da tabbatattun hujjojin da ke nuna halaccin sanya wadancan kalmomi na ‘amin’ da ‘ta’ala,’ a cikin yi ko amsa sallama. Allah Ta’ala nake roko Ya sanya wannan al’amari ya kasance don neman yardarSa ne.
Na yi wannan tsokaci ne saboda jan hankali kan abin da a ganina, ana daukar shi ba a bakin komai ba, kila domin an saba da shi, tun kaka-da-kakanni, alhali ba su ake kallo cikin aiwatar da umarni ko hani a addini ba, sai dai a kallo tushe – wato abin da ya danganta da Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam).
A takaice, sallama ita ce gaisuwar da Musulmi suke yi a tsakanin junansu wajen gaisuwa a yayin da suka hadu da juna. Gaisuwar da Musulunci ya yi musu nuni da ita – wato ‘Assalaamu alaikum’ ba ‘ina kwana’ ko ‘ina wuni’ ba, ko abin da ya yi kama da haka na al’adunsu. A dunkule, ita wannan gaisuwa, kodayake ba kanta mukalar za ta gudana kacokan ba, tana nufin aminci ne a tsakanin Musulmi. Shi wannan aminci, in dai aka yi amfani da ita sallamar, kamar yadda Manzon Allah (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya fada, aminci ne da bai kamata a samu wata cutarwa a tsakanin wadanda suka yi wa junansu ita ba.
Da farko dai Allah (Ta’ala) Yana cewa, a cikin LittafinSa Alkur’ani: “Kuma idan an gaishe ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, ko kuwa ku mayar da ita…” (Nisa’i, aya ta 86. (A gaisuwa idan aka ce muku, ‘Assalamu alaikum’ ko ‘assalamu alaikum wa rahmatullah’ ko ‘assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh,’ ku mayar da cewa, “Wa’alaikumus salamu’ ko ‘wa’alaikumus salamu wa rahmatullah’ ko ‘wa’alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh,” ko ku mayar kamar yadda aka yi muku da farko, – wato ku ma ku ce, ‘assalaamu alaikum’.) – Alkur’ani Mai girma da kuma Tarjamar ma’anoninsa zuwa harshen Hausa, shafi na 133, na Shaikh Abubakar Mahmud Gumi.
Malamai sun ce mutum na iya cewa, ‘Salamun alaikum…,’ wajen farawa.
Abu Umarata Albarra’u bin Azib, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya umurce mu da abubuwa bakwai… (cikinsu) sai ya ambaci, “…da kuma watsa sallama (a tsakaninmu).” Bukari da Muslim suka ruwaito shi. Kuma wannan lafazin, daya ne daga cikin ruwayoyin Buhari.
Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “(Wallahi), ba za ku shiga Aljanna ba, har sai kun yi imani; ba za ku yi (samu tabbataccen) imani ba, har sai kun so junanku; shin ba na shiryar da ku ga wani abu da idan kuka aikata shi, za ku so junanku ba?” (Ba shakka sahabbai za su ce suna so). Sai ya ce, “Ku watsa sallama a tsakaninku.” Muslim ne ya ruwaito shi. Ashe manufar sallama ita ce aminci ya watsu a tsakanin al’umma, ba cuta, ko cutarwa. (Don neman karin bayani, sai a nemi littattafan da suka yi magana kan tasirin sallama a tsakanin Musulmi).
An samo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Lokacin da Allah Ya halicci Adamu (Alaihis Salam), sai Ya ce masa, ‘Tafi ka yi sallama ga wadancan (wani gungun Mala’iku suna zaune), ka saurari abin da za su gaishe ka da shi, saboda ita (gaisuwar sai ta kasance) gaisuwarka ce da kuma gaisuwar zurriyyarka.” Sai ya tafi ya ce (musu), “Assalamu alaikum.” Sai suka ce, “Assalamu alaika wa rahmatullah.” Wato suka kara masa da “wa rahmatullah.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
A bayaninsa kan yadda ake yin sallama, Imam Ibn Zakariyya Yahya bin Sharf Annawawiy ya ce, “An so ga wanda zai fara sallama ya ce: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullaahi wa barakatuh.’ Sai ya gabatar da lamirin jam’i ko da wanda aka yi wa sallamar mutum guda ne. Shi kuma wanda zai karba (ya mayar), sai ya ce: ‘Wa’alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh.’ Sai ya zo da ‘wa’ ta adafi, a cikin fadinsa – wa’alaikum….”
Imran bin Husain (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Wani mutum ya zo ga (majalisar) Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya ce: ‘Assalamu alaikum.’ Sai (Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam) ya mayar masa, sannan sai (mutumin) ya zauna. Sai (Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Goma.”
Sai wani (mutumi na biyu) ya zo, sai ya ce: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullah.’ Sai (Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam) ya mayar masa, sannan sai (mutumin) ya zauna. Sai (Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Ashirin.”
Sannan sai wani (mutum – na uku) ya zo, sai ya ce: ‘Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.’ Sai (Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam) ya mayar masa, sannan sai (mutumin) ya zauna. Sai (Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Talatin.” Abu Dawuda da Tirmizi suka ruwaito Hadisin. Imam Tirmizi ya ce, ‘Hadisi ne mai kyau.’
A’isha, (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce mini, ‘Ga Jibrilu yana miki sallama.’ Sai na ce, “wa alaihis salam wa rahmatullahi wa barakatuh.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Za mu ci gaba