Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Usman Baba, ya ba da umarnin tsaurara matakan tsaro a yayin da al’ummar Musulmin ke bikin Idin Sallah Karamah.
Usmana Baba, ya kuma tura dubban jami’an rundunar don tabbatar da cikakken tsaro a lokacin bukukuwan Sallah.
- Dalilinmu na Sallar Idi ran Laraba —Dahiru Bauchi
- Abubuwan da ake so a aikta a Karamar Sallah
- Yadda aka yi Sallar Idi a Saudiyya
- Ndume ya soki Gwamnonin Kudu kan hana yawon kiwo
“Ya fahimci kalubale na addabar fannin tsaron kasa, amma ya ba da tabbacin cewa kalubalen ba su fi karfin rundunar ba,” inji sanarwar da Rundunar ta fitar ta bakin kakakinta, Frank Mba.
Ya kuma garagdi jami’an su gudanar da ayyukansu bisa kwarewa da kare hakkin bil Adama a bakin ayyukan nasu.
Sanarwa ta ce matakan za su ci gaba da dorewa har zuwa bayan bukukuwan sallar a domin tabbatar da tsaro da kare lafiyar al’umma.