Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), Shaikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ya bukaci Musulmi mawadata su tallafa wa mabukata musamman a wannan lokaci da Babbar Sallah ke karatowa.
Shaikh Jingir ya ce ’yan Najeriya da dama na cikin mawuyacin hali kuma suna bukatar taimako don gudanar da bukukuwan sallar wadda za a yi ranar Juma’a 30 ga watan Yuli.
“A yayin da Eid-el-Adha ya karato, wadanda suka samu damar yin layya su yi kokarin raba wa wadanda ba su samu ikon yin ba” inji malamin.
A ganawarsa da manema labarai a Jos babban birnin jihar Filato, Shaikh Jingir ya kwadaitar da Musulmi su yi azumi a cikin kwanaki tara na farkon watan Dhul Hajj don samun dacewa falalar kwanakin.
Ya kkuma kirayi ’yan Najeriya su yi wa kasar addu’ar samun zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaba don samun waraka daga kalubalen da take fuskanta.