✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saliyo: Masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun kashe ’yan sanda 6

Fararen hula biyu sun rasu a tarzomar da ta barke a kasar.

’Yan Sanda shida ne suka rasu sakamakon zanga-zangar da ake gudanarwa saboda tsadar rayuwa a kasar Saliyo.

Gwamnatin kasar Saliyo to bayyana a ranar Alhamis cewa ’yan sanda biyun an kashe su ne a Freetown, babban birnin kasar, yayin da aka kashe uku a birnin Kamakwie, sai dayan da aka kashe Makeni.

Shugaban ’yan sandan, Insfekta William Fayia, ya ce akalla fararen hula biyu sun mutu bayan ’yan Sandan a birnin Freetown.

Gwannatin kasar dai a baya ta ce ana samun asarar rayuka sosai sakamakon zanga-zangar, sai dai ba ta fadi adadin ba.

Sai dai ta ce hakan na faruwa ne sakamakon daruruwan masu zanga-zangar da ke jefe-jefe da kone tayoyi.

Zanga-zangar kasar dai ta balle ne don nuna bacin ran ’yan kasar kan tabarbarewar tattalin arziki, da talauci da sauran matsaloli.

A ranar Laraba ne dai aka rufe hanyoyin sadarwar yanar gizo a kasar da kuma sanya dokar takaita zirga-zirga daga karfe 3:00 na rana don kashe kaifin zanga-zangar.