✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salisu Yusuf ya zabi kyaftin din Super Eagles

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke yin wasanninsu a gida (home base) Salisu Yusuf a shekaranjiya Laraba ne ya zabi kyaftin din…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles da ke yin wasanninsu a gida (home base) Salisu Yusuf a shekaranjiya Laraba ne ya zabi kyaftin din dai zai jagoranci kungiyar.

Kocin ya zabi golan kungiyar Ifeanyi Ubah Ikechukwu Ezenwa ne a matsayin kyaftin.  Haka kuma Ezenwa ne golan Super Eagles.  Ana sa ran shi zai jagoranci kungiyar a wasan share fagen zuwa gasar cin kofin Afirka na masu yin kwallo a gida (CHAN) da zai gudana a ranar 11 ga watan gobe a tsakanin Super Eagles da Jamhuriyar Benin.

Wannan shi ne karo na 5 da ake gudanar gasar cin kofin Afirka na ’yan kwallon da ke buga kwallonsu a gida (CHAN).  Kuma ana sa ran a wannan karon gasar za ta gudana ne a Kenya a tsakanin 11 ga Janairu zuwa 2 ga Fabrairun 2018 idan Allah Ya kaimu.

Tuni koci Yusuf ya gayyato ’yan kwallo 30 da yanzu haka suke samun horo a Kano don tantance wadanda za su buga masa wasa da Jamhuriyar Benin.