Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce hadimin da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sauke daga mukaminsa ya kere masu magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ta fuskar jarumta da kuma karfin hali.
A karshen makon da ya gabata ne gwamna Ganduje ya salami Salihu Tanko Yakasai daga mukaminsa na mai magana da yawun gwamnan a kafofin sadarwa na zamani.
- Kalubalen da masana’antar Kannywood ke fuskanta – Hassan Giggs
- Yajin Aiki: DSS ta gayyaci shugaban dillalan shanu da kayan abinci
- Kotu ta daure tsohon Shugaban FaransaNicolas Sarkozy
Sallamar da Ganduje ya yi wa hadimin nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan kamen da hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS ta yi wa Salihu kan abin da wasu ke ganin cewa kamun na da babbar nasaba da caccakar gwamnatin Shugaba Buhari da ya yi na cewa ta gaza magance matsalar tsaro a kasar.
Da wannan madogara ce tsohon gwamnan Jigawa cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce jarumtar da Salihu ya nuna ta kiran gwamnati a kan gaskiya ta tabbatar ya kyakkyawan gado wurin mahaifinsa, Alhaji Tanko Yakasai wajen fada wa kowace gwamnati gaskiya ko mai dacinta.
Ya ce, “Salihu jarumi ne kamar mahaifinsa wanda a kullum yake tsayuwar daka ga shugabanni masu taurin kai.”
“Ya kamata gwamnati da hukumomin tsaro su bayar da kulawa sosai a kan sha’anin da ya danganci tunzura ’yan siyasa da fusatattun matasa ke yi.”
“Ya kamata a ce tuni masu lura da sha’anin tsaro sun hankalta da irin akidar siyasa da Salihu ya rika da za ta agaza musu wajen magance fushinsa.”
“Mahaifin Salihu, Alhaji Tanko Yakasai, ya shafe tsawon rayuwarsa wajen taka wa masu rike da madafan iko burki ta hanyar fada musu gaskiya tun daga lokacin mulkin zuwa ga Sarakunan Gargajiya da kuma shugabannin da jagoranci kasar bayan samun ’yanci da suka hada da na soji da na fararen hula.”
“Alhaji Tanko Yakasai ya sha dauri sau tari wanda shi kansa bai damu da ya rike adadin lokutan da aka daure sa ba saboda sukar gwamnati da zarar ta yi abin da yake ganin bai dace ba.”
“Saboda haka wannan shi yake nuna cewa fada wa gwamnati gaskiya gado ne Salihu ya yi wanda a jinin mahaifinsa yake na ambata wa gwamnati gaskiya komai dacinta.”
“A yanzu kamata ya yi Shugaba Buhari ya yi alfahari da Salihu wajen bin sahunsa na jarumta da karfin halin fada wa gwamnati gaskiya.”
“Babu shakka a yanzu Salihu ya rasa aikinsa kuma albashinsa ya yanke saboda karfin halin akidarsa, sai dai hakan ya kara daga martabar asalinsa da kuma gidan da ya fito kuma hakan ya nuna cewa sha bamban da irinsu Femi Adesina da Garba Shehu masu yin kurum tare zubawa gwamnati idanu idan ta aikata ba daidai ba.”
“Idan har fargabar cin mutunci ko dauri a gidan yari basu gaza hana mahaifinsa fada wa gwamnatin gaskiya ba, to babu dalilin da za su iya dakatar da Salihu Yakasai wajen kwaikwayon gwagwarmayarsa ba,” in ji Lamido.
Aminiya ta ruwaito cewa, ma’abota dandalan sada zumunta musamman Twitter da Facebook sun yi ta tayar da kura a kan cewa an kama Salihu ne wanda aka fi sani da Dawisu saboda sukar gwamnatin jam’iyyar APC a dukkan matakai da cewa ta gaza sauke mafi girman nauyi da rataya a wuyanta na tsare rayukan al’umma.
Dawisu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a bayan rahoton sace dalibai mata fiye da 300 a Makarantar GGSS Jangebe da ke Jihar Zamfara, ya ce gwamnatin APC ta gaza kuma mafi a’ala shi ne ta yi murabus.
A dalilin haka ne gwamnatin Jihar ta bakin Kwamishinan Labarai, Muhammad Garba, ta sanar da sauke shi daga mukaminsa a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar kan sukar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Garba ya ce sallamar wacce ta fara aiki nan take na zuwa ne sakamakon yadda Salihu kasancewarsa jami’in gwamnati yake ci gaba da furta lafuzan da suka sha bamban da na matsayin gwamnatin da yake yi wa wakilci.