Ga masu hannu da shuni
Salam Aminiya, don Allah masu hannu da shuni ku tallafa wa masu kananan karfi musammamma ’yan gudun hijira wadanda suke a sansani daban daban na kasar nan da ma wadanda ke kasashen makwabta, albarkacin watan Ramadan, don duk wanda ya jikan wani Allah Zai jikansa.
Daga Alhaji Umar Foreber Gashua 08108003333
Kira Ga ’yan
Najeriya
Edita ka ba ni dama in yi kira ga ’yan Najeriya, kowa ya boye katin zabensa kamar yadda yake boye kudi don zabe na gaba watau na 2019. Hakan ne zai ba mu damar sake zabo shugabanni nagari kamar yadda muka yi a bana. Na gode.
Baban Usman Katsina
Jinjina ga dangote
Allah Ya sa wannan yunkuri na kafa masana’antu da tallafa wa manoma, da Aliko dangote da gwamnatin Jihar Jigawa suke kokarin yi ya kai ga gaci.
Daga Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau. 08069807496
Allah Ya sa mu dace
Salam Editan Aminiya! Muna mika kokon bararmu ga Allahu Subuhanahu Wata’ala da Ya karbi Ibadun da za mu gudanar a wannan wata mai albarka na Ramadan. Kazalika, muna rokon Allah Ya ba mu damina mai albarka da zaman lafiya mai dorewa.
Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna 08024122559
Ga Shugaba Buhari
Salam, Edita don Allah ku isar mini da sakona ga sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya yi daidai da ya sa aka mayar da rundunar sojojin Najeriya Maiduguri.
Daga Hussaini Mikah Rijau, Jihar Neja.
Haba Aminiya!
Haba jaridarmu Aminiya, a ’yan kwanakin nan kun rage yawan sakonnin da kuke bugawa a jaridarmu, kuma ga shi masu karanta jaridarku suna kara yawa. Ina kira ga Editan shafin wasikunmu da ya kai kukanmu ga Edita don a kara yawan sakonninmu da ake bugawa.
Daga Nazifi a garin da ko da me ka zo an fi ka wato Kanon dabo.
A kara wa ’yan sanda albashi
Aminiya ki mika min sakona ga shugaban kasa Muhammadu Buhari don Allah Ya duba albashin ’yan sanda watau security. Albashinsu bai taka kara ya karya ba shi ya sa suke cutar mutane. Wasu gidansu babu abinci babu kuma kudin saye don haka dole su takura wa mutane. Don Allah ka duba halin da suke ciki kuma ka janye soja daga kan hanya don ya wulakanta a idon jama’a. Don Allah shugaban kasa ka dubi korafin jama’a kuma ka share musu hawaye.
Daga Fisabilillahi Kwanar dangora, Kano
Aminiya ta cancanci yabo
Editan Aminiya a gaskiya yanzu jaridarku ta Aminiya tana neman tserewa sa’o’inta ganin yadda take fitar da labarai na gaskiya babu karya kuma babu son kai ko nuna fifiko na addini ko yare. Sannan ga filin wasiku da kuka ware domin talakawa irinmu. Mu kam sai dai mu yi godiya da kuma addu’ar Allah Ya kara daukaka kamfanin Aminiya, amin.
Daga Yahaya Ahmed Jabo Kafin Hausa Jigawa 08026392800
Allah Ya shiryi marasa azumi
Salam ma’aikatan Aminiya, Allah Ya saka muku da alheri. Allah Ya shiryi maza da mata wadanda ba sa azumi ba tare da wani dalili ba.
Daga Nana Khadijat Adon Mata 07068785616
Sako ga Gwamnan Kano
Aminiya, a mika min sakona ga mai girma sabon Gwaman Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje. A bara na je Jihar Taraba na samu wata Kirista da ta karbi kalmar shahada kuma ta samu miji ta yi aure. Sai dai karamar Hukumar kiru ta nuna za ta taimaka mata amma har yanzu shiru kake ji. Bayan haka akwai wata ita ma da take so ta Musulunta sai dai ina so mai girma Gwamna ka sa baki a maganar, ka taimaka kamar yadda ka saba yin taimako a kan yada sakon Allah don ganin an tallafwa irin wadannan da ke Musulunta. Allah Ya yi mana jagora.
Daga 08125555569 ko 09033322295
Fatan alheri
Salam Edita, ina yi wa Musulmin duniya murnar shigowar wata mai alfarma watau watan Ramadan. Da fatan Allah Ya karbi ibadarmu.
Daga Adamu Kurma Dogarawa Zariya
Ga Aminiya
Edita, ban taba fashin sayen jaridar Aminiya ba amma abin mamaki ba ku taba buga sakona ko sau daya ba.
Daga Lawal Abubakar Dankama Kado Bilej 08054697173
Jinjina ga Aminiya
Assalamu Alaikum. Edita, ina roko don Allah ka isar da jinjina ga ma’aikatan Aminiya a bisa kokarin da suke yi. Allah Ya kara hazaka.
Daga Maryam Idris Metu Zariya 07038412210
Matasa ku yi hattara!
Ina kira ga ’yan uwana matasa, mu natsu, mu watsar da duk wata harkar shaye-shaye don ba shi da amfani komai a gareku. Mu tuna fa wata rana mu ne manyan gobe, masu fada aji. In mutum ya haukace wa zai saurare shi. Don haka mu yi hattara.
Daga Isah Dilwaala Abuja 07036379291