Buhari ka yi taka tsan-tsan da turawa!
Salam Edita don Allah ka ba ni dama in baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara dangane da yadda muka ga Turawan yammacin duniya ke yi masa shishshigi musaman irin gayyatar da shugaban Amurka Barrack Obama ya yi masa a makon jiya. Tabbas akwai abubuwa da dama da yakamata a rika la’akari da su kafin a amince musu dari bisa dari. Yakamata shugaba Buahari ka rika sara kana duban bakin gatari, don Turawan Yamma ba kasafai yakamata a rika amince musu ba. anfanar kasa baki daya.
Daga Aminu Abdu Ba Ka Noma Sani Mai Nagge, Kano 08028505350.
Jinjina Ga El-Rufa’i
Salam Editan Aminiya! Ku ba ni dama na mika jinjinata ga Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa yadda ya jagoranci fatattakar barayin Shanu da ke dajin Kamuku a karamar Hukumar Birnin Gwari na Jihar Kaduna. Hakika Malam Nasir El-Rufai ya cancanci yabo, Allah Ya taimake shi da taimakonSA.
Sako Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna 08024122559
Allah mun tuba!
Allah mun tuba. Ka yi mana mafita daga wadannan tashe-tashen hankulan da ke kokarin nakasa kasarmu Najeriya, musanman Arewacin Najeriya.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu, Gusau. 08069807496
Yabo ga ziyarar Buhari Amurka
Assalam, barkan ku da aiki. Hakika ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari a Amurka wani cigaba ne ga kasarmu Najeriya. Fatar mu dai Allah Ya sa ziyarar ta haifar mana da da mai Ido a Nahiyarmu baki daya.
Daga Hafizu Balarabe Gusau 07035304499
Satar shanu a Arewacin Najeriya
Assalamu Alaikum Editan Aminiya, don Allah ka ba ni dama in yi tsokaci a kan yadda ake yawan samun sace-sacen shanu da ake yi wa al’ummomin Fulani tare da kai musu hare-haren ta’addanci da wasu marasa imani ke aiwatarwa, wanda a gaskiya hakan bai dace ba kuma zalunci ne matuka. A waje daya muna jinjina wa dakarun tsaron hadin gwiwar jihohi shida wadan da suka yi nasarar kwato shanu kimanin dubu 2 daga hannun wasu barayi da ke dajin Kamuku na karamar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna. Don haka muna kira ga gwamnonin da ke da iyaka da wannan daji da su kara bada himma wurin kara samo hanyoyin da za a kawo karshen sace-sacen shanun fulani da makiyaya.
Daga Kwamared Nura Bello Daraja Kaset Gusau, Jihar Zamfara 08032558025.
Malamai ku ji tsoron Allah
Assalamu alaikum Edita, don Allah ina so ka ba ni da ma in yi jan hankali akan matsalar da ke faruwa ta Boko Haram kamar yadda Gwamnan Borno ya fadi cewa babu malaman da ke wa’azi a kan illar Boko Haram saboda haka matsalar sai kara ruruwa take yi. Kuma hakan gaskiya ne don da yawa daga cikin malamai ba kasafai suke son yin sharhi akansu ba saboda tunanin abin da ke iya faruwa. Yakamata ku sani cewa ba a mutuwa sai lokaci ya yi. Don haka akwai bukatar malamai ku fito fili ku rika sukar su gadan-gadan a hudubobinku da sauran wuraren gudanar da wa’azuzzuka don a kawo karshen wannan ta’addanci da suke yi.
Sako daga Muryar Jama’a ta hannun P.R.O Kwamared Isah Abdussalam Funtuwa.
Fatan alheri ga Aminiya
Salam Edita ina muku fatan alhairi tare da yi muku addu’ar Allah Ya daukaka gidan jaridar Aminiya. Muna alfahari da ku a kodayaushe.
Daga Muhammad Ahmad Idris a Kabuga Kano 08031818318
Jinjina ga Gwamnan Jigawa
Muna mika sakon dodiya da na ban-gajiya, ga mai girma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar dangane da ziyarar aiki da ya kai garin Hadeja na duba wuraren da ruwan sama ya yi wa barna. Muna kara jinjina masa dangane da soma aikin kawo karshen wannan matsala.
Hakazalika muna kara godiya ga mai girma Gwamna, dangane da aniyarsa ta gina makarantar koyon aikin jinya a Hadejaa, tare da mayar mana babban asibitin garin zuwa Asibitin kwararru wato (Specialist Hospital). Muna kara adduar Allah Ya taimaki wannan gwamnati, Ya ba su ikon sauke nauyin da al’ummar Jigawa ta dora muku.
Daga: Isah Ramin Hudu Hadeja. 08060353382
A yi sulhu da Boko Haram
Ina son yin amfani da wanan dama wajen bayyana ra’ayina game da wani al’amari da ke yawo a bakin ’yan Najeriya, wato maganar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi game da sulhu da’yan boko-haram. Tabbas yin hakan yana da kyau… Amma sai an kulla sosai, kada a maimaita abin da ya faru a baya, ma’ana ayi sulhu da wasu mutane, sannan shugabanin kungiyar (Boko haram) su fito, su karyata cewa ba da su aka yi sulhun ba.
Daga Bilya Tukur Bakori. 07030225194
Ina ’yan ta’addan suke?
Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi sharhi a kan ziyarar shugaban kasar Amurka Barack Obama kasar Kenya. Abin mamaki shi ne yadda kasar ta tsaurara matakan tsaro da jiragen yakin da ke ta walagigi har ya kamala ziyara amma kungiyoyin ta’addanci irin su Al-Shabab da ISIl da ISIS da Boko Haram da sauransu suka kasa yin motsi. Wannan ya nuna ashe matsorata ne.
Daga Aminu Muhammad Adamu, Nassaawa G.R.A Kano. 08035914445.