A jawabinsa na Barka da Sallah, Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima ya bukaci al’ummar jihar su kara hakuri tare da jajirce wa hare-haren ta’addanci da suke fama da su, sannan ya ce su sa a ransu cewa hare-haren na gab da zuwa karshe.
Gwamnan ya ce hukumomin tsaro na Gwamnatin Tarayya da taimakon matasa da ’yan sintiri da maharba tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno suna ci gaba da yin aiki tukuru wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a jihar baki daya.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su kara sakankancewa cewa kalubalen rashin zaman lafiya da jihar ke fuskanta, “Insha Allah yana gab da zuwa karshe, kuma zaman lafiyar da ake samu a jihar za ta dore tare samun walwala da sauran harkokin rayuwa.”
Ya kara da yin kira ga al’ummar jihar su ci gaba da nuna tausayawa da tallafa wa ’yan gudun hijira, kuma su kara zage damtse wajen yin addu’o’i da ci gaba da ba gwamnatinsa goyon baya a kokarin da take yin na sake gina garuruwa da farfado da harkokin rayuwa domin cimma nasarar sake tsugunar da mutanen da aka raba da muhallinsu. Ya yi kira ga mutanen jihar musamman wadanda aka raba da muhallinsu su bayar da goyon baya tare da maraba da masu aikin jin kai da suka fito daga ciki da wajen Najeriya, inda ya ce, ma’aikatan jin kai suna Borno ne domin taimaka wa wadanda suke cikin bukatar abinci da kiwon lafiya da muhalli da kayayyakin rayuwa don rage wa Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno nauyi.