Kwamitin Gaggawa na Tantance Makarantun jihar Sakkwato ya ce jihar na bukatar karin malamai 548 don cimma burin samar da ingantaccen ilimi a jihar.
Kwamitin wanda Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya kafa ya bayyana haka ne a rahotonsa inda ya ce ya tantance makarantu 360 a jihar.
Shugaban Kwamitin, Dokta Shadi Sabeh wanda ya gabatar da rahoton jiya a gidan gwamnatin jihar ya ce sun wayar da kan malaman da ba su kware ba su kara ilimi don bunkasa kwarewarsu ta koyarwa a jihar.