Sakatare-Janar na Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Mai, (OPEC), Muhammad Sanusi Barkindo, ya rasu.
Barkindo, wanda tsohon Babban Manajan Daraktan Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ne ya rasu ne sa’o’i kadan bayan ganawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata yana da shekara 63 a duniya.
- Mutumin da ya je aikin Hajji a kafa daga Birtaniya ya isa Makkah
- ’Yan bindiga sun kai wa ayarin motocin Buhari hari a hanyar Daura
- DAGA LARABA: Halin Da Harkar Ilimi Ke Ciki A Jihar Sawkwato
Shugaban NNPC, Mele Kyari, ya sanar a safiyar Laraba cewa, “Mun yi rashin Dokta Muhammad Sanusi Barkindo, wanda ya rasu da misalin karfe 11 a cikin dare ranar Talata, 5 ga watan Yuli, 2022.
“Wannan babban rashi ne ga iyalansa da NNPC da Najeriya da kungiyar OPEC da ma duniya baki daya; nan gaba za a sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa.”
Kafin rasuwar Barkindo a ranar Talata, Shugaba Buhari ya yi wata ganawa da shi, inda shugaban ya bayyana shi mastayin farin jakadan Najeriya.
Sanarwar bayan ganawar da kakakin Buhari, Femi Adesina, ya fitar ta ce shugaban ya ce tarihi ba zai manta da Barkindo ba, wanda yake dab da kammala wa’adinsa a OPEC.
Buhari ya bayyana shi a matsayin abin alfahari ga Najeriya a tsawon shekara shida da ya yi a matsayin Sakatare-Janar na OPEC na hudu daga Najeriya.