Sakamakon da aka bayyana zuwa yanzu na zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Ekiti, ya nuna cewa Abiodun Oyebanji na jam’iyyar APC ne ke kan gaba.
A cikin kananan hukumomin da aka bayyana sakamakonsu dai, yawan wadanda Mista Oyebanji ya lashe ya fi na sauran da babban rinjaye.
Wannan sakamako dai ya zo da ba-zata, kasancewar hasashe ya nuna cewa ba za a samu tazara mai yawa a tsakanin manyan ’yan takara uku ba – na APC da PDP da SDP.
Daga cikin kananan hukumomin da APC ta lashe har da Ido Osi, karamar hukumar dan takarar SDP, Segun Oni, ta asali.
Ga dai yadda sakamakon yake:
Karamar Hukumar Emure
APC 7728
PDP 2610
SDP 3445
Karamar Hukumar Kudu maso Yammacin Ekiti
APC 9679
PDP 4474
SDP 4577
Karamar Hukumar Ikere
APC 12086
PDP 3789
SDP 1943
Karamar Hukumar Ilejemeje
APC 4357
PDP 1157
SDP 2344
Karamar Hukumar Moba
APC 11609
PDP 3530
SDP 4904
Karamar Hukumar Efon
APC 4012
PDP 6303
SDP 339
Karamar Hukumar Ekiti ta Yamma
APC 15322
PDP 3386
SDP 3863
Karamar Hukumar Ijero
APC 13754
PDP 4897
SDP 5006
Karamar Hukumar Gbonyin
APC 11247
PDP 3947
SDP 3059
Karamar Hukumar Ekiti ta Gabas
APC 12099
PDP 5230
SDP 4982
Karamar Hukumar Ado
APC 23831
PDP 7575
SDP 15214
Karamar Hukumar Ikole
APC 16417
PDP 6266
SDP 5736