✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakamakon gasar Manyan Mata ya fito

Kamfanin Abnur Entertainment ya bayyana wadanda suka samu nasarar lashe gasar manyan mata da aka fara mako-mako da suka gabata. Abdul Amart Mai Kwashe ne…

Kamfanin Abnur Entertainment ya bayyana wadanda suka samu nasarar lashe gasar manyan mata da aka fara mako-mako da suka gabata.

Abdul Amart Mai Kwashe ne ya sanar da hakan inda ya ce, “Kamar yadda muka yi alkawarin bayyana sakamakon gasar da aka dauki mako biyu a na fafatawa ta Manyan Mata Challenge a yau.

“Bayan bin diddigi daki-daki, Alkalan gasar sun fitar da sunan wadanda suka samu nasara daga na farko zuwa na biyar. Sannan kuma daga na shida zuwa ashirin suna da tasu kyautar kamar yadda muka tsara”, inji shi.

Aminiya ta ruwaito kamfanin Abnur Entertainment, wanda shugabanta Abdul Amart Maikwashewa, wanda ake wa lakabi da Dujiman Kannywood na sanar da gasar domin sabon shirinsu.

Sharuddan shiga gasar su ne, a “lissafa sunan jarumai mata goma 11 na jikin fosta da za mu saki, wadanda za su fito a fim din na Manyan Mata.

“Lissafa sunan jarumai guda biyar maza wadanda za su fito cikin fim din.

“Na uku a bayyana darakta guda nawa za su ba da umarni kuma a lissafo su.

“Sai a bayyana marubuta nawa ne suka rubuta fim din a lissafo su.

“Sannan a karshe a bayyana wane ne forudusan fim din”, inji shi.

 

View this post on Instagram

 

Reposted from @abnur_entertainment Kamar yadda mu ka yi alkawarin bayyana sakamakon gasar da aka dauki mako biyu ana fafatawa ta MANYAN MATA CHALLENGE a yau. A madadin kamfanin Abnur Entertainment muna matukar godewa duk wadanda suka shiga wannan gasa da wadanda suka bada gudunmawa na gudanar da wannan gasa cikin Nasara. Bayan bin diddigi daki daki Alkalan gasar sun fitar da sunan Wanda suka samu nasara daga na farko zuwa na biyar. Sannan Kuma daga na shida zuwa ashirin Suna da tasu kyautar Kamar yadda muka tsara. Ga jerin Sunayen Wanda suka yi Nasara na Daya zuwa na hudu kamar haka: [email protected] 2.@1faridamafara 3.@habeeba_abdullahi 4.@real_kherleydo 5.@real_teemahprincess Garuruwan da za a sauki shirin 1.ABUJA 2.KADUNA 3.ZARIA. – #regrann

A post shared by Abdul Amart Muhammed (@abdulamart_mai_kwashewa) on