✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sakamakon gasar Firimiyar Najeriya a mako na 34

Pillars ta debi kashinta a hannu yayin da ta ta je wa Rangers International bakunta.

A yanzu bayan buga wasanni mako na 34, kungiyar Akwa United ce ke ci gaba da jan ragama a teburin gasar Firimiyar Najeriya.

Har yanzu Akwa United tana saman teburin da maki 64, bayan ta lallasa Warri Wolves ci 3-0 a karawarsu ta ranar Laraba.

Kano Pillars da ke mataki na uku a yanzu wacce a wasu makonni baya ta rika ’yar bani-in-baka a zaman saman teburin, ta hada maki 58 a mako na 34 na gasar.

Pillars wacce ake yi wa lakabi da sai masu gida ta debi kashinta a hannu yayin da ta ta je wa Rangers International bakunta, inda aka tashi wasa 2-0

Da wannan sakamako, Rangers International ta koma ta mataki na shida a teburin gasar, inda ta hada maki 55.

Ga yadda sakamakon mako na 34 da aka buga ranar Laraba a gasar Firimiyar Najeriya ya kasance:

Abia Warriors 2-1 Heartland FC

Akwa United 3-0 Warri Wolves

Rangers International 2-0 Kano Pillars

Jigawa Golden Stars 2-1 Rivers United

Lobi Stars 3-2 Nasarawa United

MFM FC 3-1 Plateau United

Sunshine Stars 0-0 Katsina United

Ga wasannin da za a buga a ranar Alhamis:

Dakkada FC vs Adamawa United

FC IfeanyiUbah vs Enyimba International

Kwara United vs Wikki Tourists