A yanzu bayan buga wasanni mako na 31, kungiyar Akwa United ce ke ci gaba da jan ragama a teburin gasar Firimiyar Najeriya.
Har yanzu Akwa United tana saman teburin da maki 57, bayan ta buga wasa babu ci a gidan Plateau United a ranar Lahadi.
Kano Pillars da ke mataki na biyu a yanzu wacce a wasu makonni baya ta rika ’yar bani-in-baka a zaman saman teburin, ta hada maki 55 a mako na 31 na gasar.
Pillars wacce ake yi wa lakabi da sai masu gida ta samu nasarar samun maki uku yayin da lallasa Lobi Stars da ci 3-0 a karawar da suka yi a Jihar Kaduna.
A wasan gaba na mako na 32, Akwa United za ta buga wasa mai zafi a gida tare da Enyimba International, yayin da Pillarsa za ta bakunta gidan Sunshine Stars.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne Katsina United ta kawo karshen wasanni 18 da Akwa United ta buga ba tare da an yi galaba a kanta ba a gasar Firimiyar Najeriya.
Tun daga ranar 14 ga watan Fabrairun bana, babu wata kungiya da ta yi nasara a kan Akwa United wacce take ci gaba da zama a saman teburin Firimiyar Najeriya a mako na 29.
Ga yadda sakamakon mako na 31 da aka buga ranar Lahadi a gasar Firimiyar Najeriya ya kasance:
Adamawa United 1-1 MFM FC
Enyimba International 1-1 Rivers United
Kano Pillars 3-0 Lobi Stars
Katsina United 3-0 FC IfeanyiUbah
Kwara United 2-0 Rangers International
Plateau United 0-0 Akwa United
Warri Wolves 2-0 Abia Warriors
Wikki Tourists 2-1 Dakkada FC
Rahotanni sun ce an dage wasan da Nasarawa United za ta fafata da Jigawa Golden Stars zuwa wani lokaci da ba a kai ga kayyade wa ba.