✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sakamakon Firimiyar Najeriya bayan wasannin mako na 35

Har yanzu Akwa United ce ke ci gaba da jan ragama a saman teburin gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) da maki 67. Kungiyar a wasanta na…

Har yanzu Akwa United ce ke ci gaba da jan ragama a saman teburin gasar Firimiyar Najeriya (NPFL) da maki 67.

Kungiyar a wasanta na mako na 35 ta samu nasarar lallasa Jigawa Golden Stars da ci 3-0 yayin karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Nasarawa wadda ta casa Sunshine Stars da ci 4-0 tana zaman ta biyu a tebutin da maki 61

Ita ma Kano Pillars wacce ake yi wa lakabi da masu gida, ta ci gaba da kare kambun zama ta uku a gasar ta bana da maki 61, bayan ta samu nasarar doke Abia Warriors da ci 1-0 a wasan mako na 35 na gasar NPFL da suka kara ranar Lahadi.

Kungiyar Eyimba wadda ta yi nasara a gida a kan Mountain of Fire da ci 2-1, ita ma ta hada maki 61 wacce take zaman ta hudu a teburin kakar bana.

Ga sakamakon wasannin mako na 35 da aka buga ranar Lahadi:

  • Enyimba International 2 – 1 Mountain Of Fire And Miracles
  • Rivers United 2 – 0 Ifeanyi Ubah
  • Akwa United 3 – 0 Jigawa Golden Stars
  • Plateau United 0 – 0 Lobi Stars
  • Nasarawa United 4 – 0 Sunshine Stars
  • Warri Wolves 1 – 0 Wikki Tourists
  • Heartland 0 – 0 Kada City
  • Adamawa United 1 – 1 Enugu Rangers International
  • Katsina United 2 – 0 Dakkada