Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya zargi kasashen Turai da yin sakaci wajen kakaba wa kasar Rasha takunkumi tun da wuri don hana ta mamayar da take yi wa kasarsa a yanzu.
Zelensky ya ce kamata ya yi a ce sun sanya takunkuman tun kafin ta mamaye kasar ta yadda za su zama na gargadi, ba na fargar jaji ba, bayan an kaddamar musu da hare-haren.
- Limanin Juma’a ya ajiye limanci don tsayawa takarar siyasa
- Buhari ya gana da Tinubu da Bisi Akande gabanin taron APC
A wani jawabinsa da aka yada ta bidiyo, Shugaba Zelenskyy ya shaida wa Tarayyar Turai cewa hatta sanya takunkumi a kan kamfanin da ke tunkuda iskar gas daga Rasha zuwa Jamus na Nord Stream 2, shi ma an yi shi a makare.
Jawabin nasa na zuwa ne bayan kasar ta Ukraine ta zargi dakarun Rasha da yi wa ’yan kasarta kimanin 400,000, ciki har da kananan yara 84, kofar rago a kasar.
A cewar Shugaban, “Game da batun Tarayyar Turai kuwa, muna godiya. Kun kakaba takunkumai, kuma sun taimaka sosai, amma sun dan zo a makare.
“Kamata ya yi a ce tun kafin ta kaddamar da hare-haren aka dauki matakan, da ba za ma ta kai ga kawo mana hare-haren ba. Akwai yiwuwar su ja da baya a lokacin,” inji Zelenskyy.
Ukraine dai ta nemi shiga kungiyar Tarayyar Turai, inda Shugaban a cikin jawabin nasa ya roke ta da ta gaggauta amincewa da bukatar tasu.
A wani labarin kuma, Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce kungiyar kawancen tsaro ya NATO za ta dauki matakin da ya dace muddin Rasha ta yi amfani da makamai masu guba a Ukraine.