Hukumar Zabe ta Kasar Libya, ta sanya haramcin takarar shugaban kasa ga Saif al-Islam Gaddafi, da ga tsohon Shugaban Kasa, Mu’ammar Gaddafi.
Hukumar ta ce Seif al-Islam na daya daga cikin ‘Yan takara 25 da ta haramtawa takara inda taki amincewa da takardun takararsu a zaben da za a yi a ranar 24 ga watan Disamba.
- An kama mahaifi kan zargin sayar da ’ya’yansa saboda bashi
- Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin rataya kan kisan kawunsu
Daga cikin wadanda suka gabatar da takardun takarar akwai Janar Khalifa Haftar wanda ya dade yana yaki domin karbe ikon kasar, yayin da kotu a Amurka ke neman sa ruwa ajallo domin fuskantar tuhumar laifuffukan yaki.
Sauran ’yan takarar sun hada da Firaministan rikon kwarya Abdelhamid Dbeiba da shugaban Majalisar Dokoki da kuma tsohon Ministan Cikin Gida, Fathi Bashagha.
Kamar yadda Rediyon Faransa ta ruwaito, mata biyu ne kacal suka gabatar da takardun su na yin takara, kuma sun hada da Laila Ben Khalifa mai shekaru 46 da Hunayda al-Mahdi.
Shugaban hukumar zaben kasar Imad al-Sayed ya ce mutane 98 suka gabatar da takardun tsayawa takarar zaben shugaban kasar.
’Yan kasar Libya miliyan 2 da dubu 800 suka yi rajistar kada kuri’a, kuma ya zuwa yanzu miliyan guda da dubu 700 sun karbi katin zaben su.
Saif al-Islam: Dan Gaddafi ya yi rajistar takarar Shugaban Libya
Makonni biyu da suka gabata ne Hukumar zabe ta bude rajistar ’yan takara a kasar Libya, inda Saif al-Islam, dan marigayi Mu’ammar Gaddafi ya yi rajistar tsayawa takarar shugaban kasar Libya a zaben watan Disamba mai zuwa.
Hukumar Zaben kasar ce ta fitar da sanarwar mai cewa Saif ya yi rajistar tsayawa takarar zaben shugaban Libya
Sanarwar ta ce “Saif al-Islam Gaddafi ya mika rajistar takararsa ta shugabancin kasa zuwa ga Hukumar Zabe a birnin Sebha,” a cewar hukumar.
Ta ce ya cika “dukkan ka’idojin da ake bukata” sannan kuma an ba shi katin jefa kuri’a na gundumar Sebha.
Wannan ne karon farko da za a gudanar da zaben shugaban kasa a matakin gama-gari a Libya ranar 24 ga Disamba bayan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta shiga tsakanin bangarorin da ke yakar juna a kasar.
A watan Yulin da ya gabata ne Saif al-Islam mai shekaru 49 a duniya ya bayyana bayan ya shafe shekaru a boye, inda ya bayyana wa jaridar New York Times sha’awarsa ta shiga siyasa.