✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saif al-Islam: Dan Gaddafi zai yi takarar Shugaban Libya

Ya cika dukkan ka’idojin da ake bukata sannan kuma an ba shi katin jefa kuri’a.

Saif al-Islam, dan marigayi Mu’ammar Gaddafi ya yi rajistar tsayawa takarar shugaban kasar Libya a zaben watan Disamba mai zuwa.

Bayanai sun ce hakan na zuwa ne bayan da a ranar Litinin Hukumar zabe ta bude rajistar ’yan takara a kasar Libya.

Wata sanarwa da Hukumar Zaben kasar ta fitar ta ce Saif ya yi rajistar tsayawa takarar ce a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce “Saif al-Islam Gaddafi ya mika rajistar takararsa ta shugabancin kasa zuwa ga Hukumar Zabe a birnin Sebha,” a cewar hukumar.

Ta ce ya cika “dukkan ka’idojin da ake bukata” sannan kuma an ba shi katin jefa kuri’a na gundumar Sebha.

Wannan ne karon farko da za a gudanar da zaben shugaban kasa a matakin gama-gari a Libya ranar 24 ga Disamba bayan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta shiga tsakanin bangarorin da ke yakar juna a kasar.

A watan Yulin da ya gabata ne Saif al-Islam mai shekaru 49 a duniya ya bayyana bayan ya shafe shekaru a boye, inda ya bayyana wa jaridar New York Times sha’awarsa ta shiga siyasa.